logo

HAUSA

AfDB na neman kasar Sin ta zuba jari a bangaren makamashi mai tsafta na nahiyar

2022-06-09 13:13:43 CMG Hausa

Bankin raya nahiyar Afrika (AfDB) na neman karin taimako daga kasar Sin, wato ta zuba jari a bangaren ayyukan makamashi mai tsafta na nahiyar.

Daniel Schroth, daraktan sashen kula da makamashi mai tsafta da ingancin makamashi na bankin, ya shaidawa Xinhua cewa, bisa la’akari da yadda kungiyar kasashe masu tasowa ke da kwarewa da gogewa a fannin makamashi mai tsafta, abu ne mai muhimmanci bankin ya karfafa hadin gwiwa da kasashen Asia, ciki har da Sin.

Ya ce sanin kowa ne kasar Sin ta fadada karfinta na samar da makamashi mai tsafta cikin ’yan shekarun da suka gabata. Yana mai bayyana shi a matsayin gagarumar nasarar da ya kamata Afrika ta yi koyi da ita.

Ya ce dimbin albarkatun makamashi mai tsafta da nahiyar ta mallaka ciki har da na ruwa da rana a fadin nahiyar, da karfin iska a wurare daban- daban na nahiyar, ya ba ta wata gagarumar dama ta hadin gwiwa da masu ruwa da tsaki a bangaren, ciki har da kasar Sin. (Fa’iza Mustapha)