logo

HAUSA

Mutuwar mutane sanadiyyar ayyukan ta’addanci ya karu a nahiyar Afrika

2022-06-09 11:16:22 CMG Hausa

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya ce yayin da adadin wadanda ke mutuwa sanadiyyar ayyukan ta’addanci ke raguwa a sassan duniya, adadin na karuwa a nahiyar Afrika.

Antonio Guterres ya bayyana haka ne jiya, yayin taron yarjejeniyar hadin gwiwa kan yaki da ta’ddanci a duniya na MDD.

A cewarsa, kungiyoyin ta’addanci kamar al-Qaida da IS da rassansu na ci gaba da karuwa a yankin Sahel, tare da kutsawa yankin tsakiya da kudancin nahiyar Afrika.

Ya ce biyo bayan ziyararsa a jihar Borno dake arewacin Nijeiya da ta kasance tungar kungiyar BH, yana da yakinin cewa, ana kan hanyar cimma sulhu tare da kara shigar da tubabbun ’yan ta’adda cikin al’umma.

Ya kara da cewa, shirin gwamnatin Nijeriya shi ne, karfafa aminci tsakanin al’umma da kuma rushe tsarin kungiyar BH na horar da mayaka. Yana mai cewa, yanzu haka, mayakan BH da suka tuba na komawa cikin al’umma, kuma jama’a ne da kansu, suka raunata ayyukan BH.

A cewarsa, ingantacciyar dabara na da muhimmanci ga tsarin yaki da ta’addanci na MDD, yana mai kira da kara mayar da hankali ga bangarorin kiwon lafiya da samar da ilimi da kariya da tabbatar da daidaiton jinsi da tsarin shari’a ga kowa da samar da tsarukan demokradiyya, ta yadda kowanne mutum zai iya bada gudummawa a cikin al’ummarsa da kasa baki daya. (Fa’iza Mustapha)