logo

HAUSA

Cinikin waje na kasar Sin ya bunkasa yadda ya kamata

2022-06-09 21:31:29 CMG Hausa

Babbar hukumar kwastam ta kasar Sin, ta fitar da sabuwar kididdiga kan harkokin cinikin waje, inda aka nuna cewa, a watan Mayun bana, jimillar kudaden shige da fice na kasar Sin ta kai dala biliyan 537.74, wadda ta karu da kaso 11.1 bisa dari. Duk da cewa annobar COVID-19 na ci gaba da yaduwa, amma harkokin cinikin waje na kasar Sin, sun bunkasa yadda ya kamata tun daga watan Janairu zuwa Mayun bana, al’amarin da ya sake nunawa duniya babban kuzari da kwarewar kasar Sin.

Kwararan shaidu sun tabbatar da cewa, tasirin annobar na gajeren lokaci ne, kana, manufar da gwamnatin kasar Sin take aiwatarwa, wato dakile yaduwar cutar da zarar an gano ta, gami da sauran wasu muhimman matakan kandagarkin yaduwar cutar da raya tattalin arziki sun taka rawar a-zo-a-gani.

Harkokin cinikin waje za su iya bayyana yadda tattalin arzikin kasar Sin yake gudana. A watanni biyar da suka gabata, kasar ta cimma tudun-dafawa wajen bunkasa cinikin waje, abun dake karfafa gwiwar duniya baki daya.

Duk da rashin sanin tabbas game da yaduwar cutar COVID-19 a halin yanzu, babban burin gwamnatin kasar Sin a fannin dakile yaduwar cutar shi ne, yin namijin kokari wajen kare rayuwar al’umma gami da lafiyarsu, da rage illolin da cutar ke haifarwa ga tattalin arziki da rayuwar al’ummar kasar. Tun daga gwamnatin kasa har zuwa kananan hukumomi, tun daga gwamnati har zuwa kamfanoni, duk dan kasar na kokarin ganin an cimma wannan burin. Kasar Sin tana da kwarewa wajen tabbatar da ci gaban tattalin arzikinta yadda ya kamata, da ci gaba da bayar da muhimmiyar gudummawa wajen samar da kayayyaki da farfado da tattalin arzikin duniya. (Murtala Zhang)