logo

HAUSA

Shugaban kasar Sin ya jaddada kare kayayyakin tarihi da al’adun gargajiya

2022-06-09 19:22:59 CMG Hausa

San Su Ci ke nan, wurin tunawa kuma tsohon mazaunin Su Xun da 'ya'yansa maza guda biyu Su Shi da Su Zhe, mashahuran mutane uku ta fannin adabi na zamanin daular Song ta Arewa (960-1127). Shugaban kasar Sin Xi Jinping, wanda ya kai rangadin aiki birnin Meishan na lardin Sichuan da ke kudu maso yammacin kasar a jiya Laraba, ya ziyarci wurin, inda ya jaddada muhimmancin kare kayayyakin tarihi da al’adun gargajiya.

Su Shi ya kuma kasance dan siyasa baya ga kwarewa a fannin adabi, wanda a tsawon shekaru 40 da ya shafe kan mukaminsa, ya dukufa wajen bauta wa al’ummar kasar.

Shugaba Xi ya sha tsamo wakoki da kalaman da Su Shi ya yi, inda ya jaddada muhimmancin yaki da cin hanci da rashawa, tare da bukatar jami’an gwamnatin kasar da su yi kokarin sauke nauyin da ke bisa wuyansu.(Lubabatu)