logo

HAUSA

Da Abokin Daka Akan Sha Gari

2022-06-09 20:07:32 CMG Hausa

Kamar yadda muke ji yau da kullum daga bakin masana, cewa babu wata kasa a duniyar nan da za ta samu cikakken ci gaba, ba tare da bunkasa yankunanta na karkara ba, muna iya ganin shaidu na zahiri don gane da hakan a nan kasar Sin.

Mahukuntan kasar Sin sun jima da fahimtar muhimmancin kawar da kangin talauci da raya karkara, a matsayin babban jigon gina kasa, tare da tabbatar da ba a bar wani bangare na al’ummar Sinawa a baya ba. Kaza lika da yake yankunan karkara na taka muhimmiyar rawa wajen gina kasa, ta hanyar samar da nau’o’in cimaka, kama daga hatsi, da kayan lambu da ’ya’yan itatuwa, gudummawar sassan na karkara na kan gaba wajen tabbatar da samar da isasshen abinci ga daukacin yankunan kasar, hakan ya sa har kullum, gwamnatin Sin ke kara azama wajen ganin yankunan karkara sun kara azamar fita daga talauci, da samun kyakkyawar rayuwa.

Bahaushe kan ce “Da ruwan ciki a kan ja na rijiya”, har kullum mahukuntan Sin na dagewa wajen ganin yankunan karkarar kasar sun samu dukkanin tallafin da suke bukata na raya sana’o’i, da inganta damammakin samar da ilimi, lafiya da sauran ababen more rayuwa.

Wannan ne ma ya sa duk da yawan ayyukan dake gaban shugaban kasar Xi Jinping, wanda kuma shi ne babban sakataren kolin JKS, ya kan ware lokuta musamman domin ziyartar yankunan karkarar kasar Sin, ya gana da jama’ar yankunan, ya ji koken su, da yanayin rayuwar su, da irin ci gaban da suka samu karkashin manufofin wanzar da ci gaba.

Wani abun birgewa game da manufar gwamnatin Sin mai ci shi ne yadda take karfafa gwiwar yankunan karkara, wajen tashi tsaye domin dogaro da kai. Cikin kalaman shugaba Xi Jinping ya taba bayyana cewa “Idan har burin mu shi ne kallon na sama da mu, muna neman a taimaka mana, muna korafin rashin samun dama kamar saura, ta yaya za mu iya samun karfin gwiwar yakar fatara?”

Ziyarar da shugaba Xi Jinping ya kai kauyen Yongfeng na lardin Sichuan a cikin makon nan, ta shaida wannan muhimmiyar manufa, domin kuwa yayin da yake rangadi a kauyen na Yongfeng, ya nazarci yadda ake kara azamar kyautata samar da kayan noma na zamani, da matakan bunkasa samar da hatsi a yankin, da ayyukan raya karkara, da matakan dakile yaduwar annobar COVID-19.

Wannan ziyara ta shugaba Xi, ta dada shaida burin mahukuntan Sin, na yin tafiyar samar da ci gaba tare da dukkanin yankunan kasar, ta yadda kowa zai ci gajiya daga alfanun manufofin kawar da talauci, da wanzar da ci gaba, da gina al’umma mai makomar bai daya ga kowa, kamar dai yadda a kan ce “Da abokin daka a kan sha gari”. (Saminu Hassan)