logo

HAUSA

Mutanen da suka rasu sanadiyyar harin da aka kai wata mujami’a a Najeriya sun karu zuwa 40

2022-06-09 10:13:28 CMG Hausa

Gwamnan jihar Ondo dake kudu maso yammacin tarayyar Najeriya, Arakunrin Rotimi Akeredolu ya bayyana cewa, adadin mutanen da suka rasa rayuka yayin harin da aka kai wa wata mujami’a dake jihar ya karu zuwa 40.

Gwamna Rotimi Akeredolu ya bayyana yayin taron manema labarai da aka shirya jiya cewa, alkaluman kididdigar da hukumar lafiya ta jihar ta fitar sun nuna cewa, kawo yanzu adadin mutanen da suka rasu sanadiyyar harin da aka kai wa mujami’ar a ranar 5 ga wata, ya riga ya kai 40, kana wasu 87 sun jikkata. Daga cikinsu kuma, 61 suna samun jinya a asibiti. Ya kara da cewa, gwamnatin jihar za ta kafa makabarta a garin Owo domin binne wadanda suka rasu yayin harin.

A ranar 5 ga wata ne wasu ‘yan bingida sun kai wa mujami’ar katolika ta St Francis ta garin Owo na jihar Ondo hari, inda mutane da dama suka rasu ko jikkata. A sanadin haka, gwamnatin jihar ta ayyana makoki na kwanaki 7 domin jimamin wadanda suka rasu yayin harin.  (Jamila)