logo

HAUSA

‘Yan wasan kwallon kafa mata ‘yan kabilar Li da Miao suna kokarin cimma burinsu a fannin wasan

2022-06-09 20:30:17 CMG Hausa

A kowace rana da safe, kungiyar ‘yan wasan kwallon kafa mata ta garin Qiongzhong na kabilar Li da Miao mai zaman kansa dake lardin Hainan ta shiga aikin horaswa har na tsawon awa guda. Bayan horaswar, mata  membobin kungiyar sun tafi zuwa makarantunsu don yin karatu.

Garin Qiongzhong na kabilar Li da Miao mai zaman kansa gari ne mai fama da talauci a lardin Hainan na kasar Sin, gwamnatin yankin ta samar da kudi don nuna goyon baya ga raya kungiyar wasan kwallon kafan matan a fannonin bada ilmi, da samar da abinci da wurin kwana, ta hakan aka sassauta matsalar zaman rayuwa ta membobin kungiyar.

Wadannan mata wato membobin kungiyar wasan kwallon kafa mata ta garin Qiongzhong ba suyi aure ko barin garin don neman aiki a waje kamar sauran matan garin ba, sun zabi hanyar yin rayuwa ta musamman. Bayan da aka kafa kungiyar wasan kwallon kafa mata ta garin Qiongzhong a shekarar 2006, matan garin fiye da 30 sun shiga jami’a domin buga wasan kwallon kafan.

A garin Qiongzhong, a sakamakon fama da talauci da rashin bude ido zuwa waje, mata kalilan ne suka samu damar shiga makarantar sakandare, har ma basu taba tunawa da samun damar shiga jami’a ba.

Bayan da kungiyar ta yi kokarin horaswa har na tsawon wasu shekaru, kungiyar ta cimma wasu nasarori a gasannin wasan kwallon kafan a matakin kasa tun daga shekarar 2015 zuwa 2017 a jere, kana kungiyar ta ciyo kofin Gothia wato gasar wasan kwallon kafa ta matasa mafi girma ta duniya.

Huang Weiwei tauraruwa ce ta kungiyar wasan kwallon kafan matan, wadda ta taba zama ‘yar wasan kwallon kafa mafi kwarewa a cikin ‘yan wasan kwallon kafa mata matasa na duniya. Yanzu tana shekaru da 14 da haihuwa, kana tana yin karatu a wata makarantar midil. Gidansu yana da nisa daga makarantar da take, mahaifinta yakan kai ta zuwa makarantar takan hau keken babur har na tsawon awa daya da rabi.

Lokacin da Huang Weiwei tana da shekaru 8 da haihuwa, wani mai horaswa ya zo makarantar firamare ta Huang Weiwei, da ganinta ya fahimci akwai kyakkyawar makoma a tattare da Huang Weiwei game da wasan kwallon kafa. Tun daga wancan lokaci, zaman rayuwar Huang Weiwei ya fara samun babban canji.

An kai ta zuwa wata makaranta mafi kyau a cikin gari, inda ta samu ilmi da kuma horo a wasan musamman a dukkan fannoni.

Ta taba ta zuwa kasashen Sweden, da Denmark, da kuma Norway, kana ta ta je biranen Shanghai, da Beijing, da Hangzhou don yin horaswa ko yin gasanni, a cewarta, ta bude idonta ta hanyar buga wasan kwallon kafa. Ta ce, bayan da ta dawo, kungiyar tasu tayi kokari, kungiyar ta samu wasu nasarori.

Mahaifiyar Huang Weiwei Wei Zhuqin ta bayyana cewa, Huang Weiwei ce yarinya daya kawai da ta buga wasan kwallon kafa a kasashen waje, iyayenta suna yin alfahari da ita.

Huang Weiwei ta ce, tana son samun damar shiga jami’a ta hanyar buga wasan kwallon kafa, tana son za ta shiga kungiyar wasan kwallon kafa mata ta kasar Sin a wata rana.

Kafin Huang Weiwei ta fara buga wasan kwallon kafa, iyayenta basu san ka’idojin wasan ko daya ba. Yanzu sun zama masu sha’awar Huang Weiwei kan wasan kwallon kafa. Sun kalli gasannin da Huang Weiwei ta buga ta telebijin. Kana sun taba tafiya zuwa cibiyar garinsu don kallon wata gasar da Huang Weiwei ta halarta tare da nuna goyon baya gareta.

A shekarar 2019, an gudanar da gasar cin kofin kasa da kasa ta wasan kwallon kafa a garin Qiongzhong dake lardin Hainan, inda kungiyoyin wasan 21 daga kasashe da yankuna 17 dake kunshe ‘yan wasa kimanin 400 suka halarci gasar. Mutane mazauna garin fiye da dubu 10 sun zo don kallon gasar, kana masu sha’awar wasan kwallon kafa na duniya sun fara gano wannan gari, tare da gano akwai wata kungiyar wasan kwallon kafan mata ta garin.

A halin yanzu, an kafa wata kungiyar wasan kwallon kafa ta kwararru a lardin Hainan, wadda ta nemi hadin gwiwa tare da makarantun lardin, da samar da kos ta koyar da fasahohin wasan kwallon kafa ga daliban makarantu.

Chen Xin mai shekaru 28 da haihuwa, itace ‘yar wasa da ta shiga tawaga ta farko ta kungiyar wasan kwallon kafa mata ta garin Qiongzhong lokacin da aka kafa ta. Yanzu ta zama wata malama mai koyar da fasahohin wasan kwallon kafa a makaranta. Ta bayyana cewa, ta shiga jami’a don koyon ilmin wasanni. Yanzu ta tsaida kudurin komawa garinta don zama wata malama mai koyar da fasahohin kwallon kafa. Ta ce ta yi sa’a domin wasan kwallon kafa ya taimaketa wajen gano mene ne burinta a zaman rayuwarta. A halin yanzu, tana kokarin samar da gudummawa kan sha’anin bada ilmi, musamman wasan kwallon kafa.

A shekarun baya baya nan, kasar Sin tana kokarin raya sha’anin wasan kwallon kafa a dukkan kasar, musamman samar da damar koyarwa yara fasahohin wasan kwallon kafa a makarantu. Kana kasar Sin za ta kafa tsarin yin gasannin wasan kwallon kafa na matasa na kasar, don horar da karin matasa da kwararru a fannin buga wasan kwallon kafa.

Ma’aikatar bada ilmi ta kasar Sin, da hukumar kula da harkokin wasanni ta kasar, da kuma kungiyar hadin gwiwa ta wasan kwallon kafa ta kasar sun gabatar da shirin gudanar da gasar wasan kwallon kafa ta matasa ta kasar Sin wato the China Youth Football League (CYFL) na kakar shekarun 2022 zuwa 2024, dukkan kungiyoyin wasan kwallon kafa na matasa na kasar Sin suna iya yin rajistar halartar gasar, ko makarantu, ko kwalejojin horaswa, ko kungiyoyin kwararru, dukkansu suna iya yin rajistar.

A cewar jami’i mai kula da wannan batu, ta hanyar yin gasar, za a sa kaimi ga karin matasan kasar Sin su zabi buga wasan kwallon kafa, da kara samun damar neman masu kwarewa a cikinsu.