logo

HAUSA

Sin Ta Yi Kira Da A Kiyaye Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali A Yankin Tsakiyar Afirka

2022-06-09 10:40:43 CMG HAUSA

Dai Bing, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD ya yi kira da a kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin tsakiyar Afirka.

Dai Bing ya fadi haka ne yayin wani taron kwamitin sulhu na MDD kan batun yankin tsakiyar Afirka da aka yi a jiya, inda ya kuma nuna cewa, tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin na tsakiyar Afirka, yana amfanawa cikakken tsaron nahiyar Afirka. Kuma kasar Sin na tsayawa tsayin daka wajen goyon bayan kasashen da ke yankin da su yi kokarin kiyaye ikon mulkin kasa da cikakkun yankunansu. Ya ce wajibi ne kasashen yankin masu ruwa da tsaki su daidaita sabani ta hanyar diplomasiyya da siyasa, a kokarin tabbatar da hadin kansu da kwanciyar hankali a yankin.

Dai Bing ya kara da cewa, ya kamata kasashen duniya su kara ba da tallafin kudi da na fasaha ga kasashen yankin domin yaki da ta’addanci, da mara musu baya wajen tsara shirin kwance damara, a kokarin dakile yaduwar ta’addanci. Haka kuma ya kamata a goyi bayan kasashen yankin wajen kyautata kwarewarsu ta tafiyar da harkokin kasa, da taimakawa al’ummomi fita daga kangin talauci, da kuma daidaita batun haka da cinikin albarkatun halittu ba bisa doka ba, ta yadda za a kawar da tushen rikice-rikice. (Tasallah Yuan)