Ta Yaya ‘Yan Siyasan Amurka Za Su Yi Karin Bayani Kan Karyarsu Kan Xinjiang?
2022-06-08 12:10:11 CMG HAUSA
Kwanan baya, jawabin wata tsohuwar jakadar kasar Amurka a kasar Sin da kafofin yada labaru suka gabatar, ya sake sanya mutane sun kara sanin halayyar wasu Amurkawa. An ruwaito cewa, Sheila Carey, karamar jakadar Amurka mai kula da tattalin arziki da siyasa a birnin Guangzhou da Andrew Chira, sun yi karin bayani kan makarkashiyar Amurka kan batun Xinjiang a wata liyafa a asirce a shekarar 2021, a yunkurin neman samun goyon bayan kamfanonin Amurka, inda suka ce, “Lallai ba matsala a jihar Xinjiang. Mun san haka, amma muna kara gishiri kan batun wai tilastawa a yi aiki a Xinjiang, da kisan kiyashi a jihar, tare da sukar kasar Sin kan batun hakkin dan Adam. Nufinmu shi ne jefa gwamnatin Sin cikin mawuyacin hali baki daya.”
Matakan da Amurka take dauka kan batun Xinjiang sun wuce zaton mutane, alal misali, kirkiro karya, da kara gishiri da kuma shafa wa kasar Sin bakin fenti. Turawa kan ce, idan ka yi karya sau daya, to, za ka ci gaba da yin karya sau dari 1. Amma karya ba ta musunya hakikanin halin da ake ciki a Xinjiang ba, inda ake samun kwanciyar hankali da wadata, sa’an nan mazauna wurin suna jin dadin zamansu.
Alkaluman da mahukuntan jihar Xinjiang suka gabatar sun nuna cewa, a watan Janairu zuwa Mayu na bana, an samar da sabbin guraben aikin yi dubu 263 a Xinjiang, wanda ya kai kashi 57.17 cikin kashi 100 bisa jimillar sabbin guraben aikin yi a bana. Yayin da ake fuskantar barazana wajen raya tattalin arziki da kuma yaki da annobar COVID-19 a kasar, Xinjiang ta yi kokari sosai domin cimma wannan manufa. Al’ummomin Xinjiang masu yawa sun yi nuni da cewa, suna aiki tukuru domin samun zaman rayuwa mai kyau, ba wanda ya tilasta musu.
Wasu suna shakkar cewa, me ya sa Amurka ta mai da hankali kan musulman da ke zama a Xinjiang kawai, duk da cewa, musulmai fararen hula masu yawa da ba a iya kidaya yawansu ba sun rasa rayukansu cikin yake-yaken da Amurka ta gudanar da sunan “yaki da ta’addanci”? Wajibi ne ‘yan siyasan Amurka su yi karin bayani kan karyarsu kan Xinjiang. (Tasallah Yuan)