logo

HAUSA

Taron sadarwa na duniya ya bukaci a rage gibin fasahar zamani tsakanin kasa da kasa

2022-06-08 11:05:26 CMG Hausa

An kaddamar da babban taron raya fasahar sadarwa na duniya karo na 8 a birnin Kigali, fadar mulkin kasar Ruwanda a ranar Litinin 6 ga wata, inda wakilai mahalarta taron suka yi kira ga kasashen duniya da su hada kai domin rage gibin fasahar zamani dake tsakanin kasa da kasa.

Babban sakataren kawancen sadarwar na duniya Zhao Houlin, ya bayyana yayin bikin kaddamar da babban taron cewa, a halin da ake ciki yanzu, kusan al’ummun kasa da kasa biliyan 5 suna amfani da yanar gizo, ana iya cewa, bil adama sun riga sun samu babban ci gaba, amma saura kusan biliyan 3 sun kasa yin amfani da yanar gizo, daga cikinsu, yawanci suna rayuwa ne a kasashe masu tasowa ko kauyukan dake fama da kangin talauci.

A nasa bangaren, babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya yi tsokaci cikin jawabin da ya gabatar yayin bikin kaddamar da babban taron ta kafar bidiyo cewa, duk da cewa, an gamu da matsala da kalubale yayin da ake kokarin tabbatar da dauwamammen ci gaba, amma fasahar zamani tana taka babbar rawa kan aikin.

Ana gudanar da babban taron ne tsakanin ranar 6 zuwa 16 ga wata, wanda ya samu mahalarta sama da dubu daya da suka zo daga kasashe da yankuna fiye da 100, kuma wannan ne karo na farko da aka shirya babban taron a nahiyar Afirka, inda za a tattauna batutuwan dake shafar sabbin dabarun raya kasa ta hanyar kirkire-kirkire, da sabbin hanyoyin gudanar da cudanya da hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa, da fasahohin zamanin da za a yi amfani da su don cimma burin samun ci gaba mai dorewa. (Jamila)