logo

HAUSA

Abinci Shi Ne Tushen Rayuwa

2022-06-08 17:40:40 CMG Hausa

MDD da hukumomin kasa da kasa su kan fito da jerin tsare-tsare da manufofi, baya ga wasu ranaku da ake kebewa a duk shekara, don nazartar irin nasarori da ma akasin haka da bangaren aikin samar da abinci a duniya ke fuskanta. Sai dai annobar COVID-19 da ke ci gaba da addabar sassan duniya, ta haifar da illoli da sauran matsaloli ga bangaren samar da abinci a duniya, inda alkaluma ke nuna cewa, kusan kashi 10% na yawan al’ummar duniya na fuskantar yunwa. Sai dai yayin da wasu kasashe ke nuna halin ko’in kula kan wannan lamari, ita kuwa kasar Sin a matsayinta na babbar kasa mai tasowa, wadda ke sauke nauyin dake bisa wuyanta, wajen ganin duniya ta amfana da duk wata irin kwarewa da fasahohinta, musamman kasashe masu tasowa, baya ga taimakawa kasashe masu tasowa, wajen inganta ayyukansu na noma ta hanyoyi daban daban.  

Kasashen Afirka da dama, kamar Najeriya sun amfana da irin fasahohin noma da ma irin shinkafa mai inganci daga kasar Sin, matakan da suka taimaka matuka wajen kara yawan shinkafar da ake nomawa a irin wadannan kasashe fiye da shekarun baya.

Bayanai na nuna cewa, daga lokacin da aka kaddamar da hadin gwiwar kasashe masu tasowa karkashin hukumar samar da abinci da gona ta MDD wato FAO, a shekarar 1996, ya zuwa yanzu, kasar Sin ta tura masana ayyukan gona da injiniyoyi kusan 1100 zuwa kasashe sama da guda 40 na nahiyar Afrika, da Asiya, da kudancin Pacific, da yankin Caribbean da sauran sassan duniya. Abin da ya kara nuna muhimmancin da kasar Sin ke bayarwa ga batun samar da abinci, kasancewarsa tushen rayuwa, sabanin yadda wasu kasashe ke buya abinci, inda suke amfani da shi a matsayin makami na haifar da yunwa a duniya.

Karkashin kulawar hukumar FAO, kwararrun kasar Sin sun yi aiki tukuru wajen daga matsayin fasahohin ayyukan noma sama da 1000 a kasashe masu yawa a fannoni daban daban na aikin gona, da kiwon dabbobi da halittun ruwa, da noman rani, da kuma sarrafa kayan amfanin gona, lamarin da ya taimaka wajen bunkasa karuwar samar da irin shuka a gonaki daga kaso mai tarin yawa. Haka kuma kusan manoma 100,000 a kasashen duniya ne suka samu irin wannan horo daga masanan na kasar Sin.

A gabar da duniya ke fama da tasirin annobar COVID-19, baya ga matsaloli na sauyin yanayi da shi ma ke yiwa bangaren aikin gona illa ta wasu fannoni. Sai dai kamar kullum, bikin magaji ba ya hana na magajiya, ma’ana hakan ba zai hana masu ruwa sa tsaki daukar matakan da suka dace na ganin an wadata duniya da abinci ba.

Bayanai na nuna cewa, akwai tarin jama’a a sassan duniya dake fama da yunwa sakamakon wasu matsaloli ko dalilai ko matakan kashin kai da wasu kasashen yamma suka dauka. Matakai da tsare-tsare da kasar Sin ke bijiro da su karkashin hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka, sun taimaka matuka wajen kara samar da abinci da ma dabarun noma kala-kala a sassan nahiyar. Masana na cewa, kasashen Afrika za su iya amfani da huldar dake tsakanin Sin da nahiyar, wajen kawo gagarumin sauyi a tsarin aikin gona, da magance yunwa, da karancin sinadarai masu gina jiki, da kuma habaka tattalin arzikin mazauna karkara.

A cewar shugaba Xi Jinping na kasar Sin, dalilin da ya sa JKS mai mulkin kasar ke samun cikakken goyon baya daga al’ummar kasar shi ne, tana tsayawa kan kokarin tabbatar da ingancin rayuwar jama’a, musamman manoma. Wannan na nuna cewa, idan har ana son wadatar da kasa da abinci, ya kamata mahukunta su taimakawa manoma don su samu karin kudin shiga, da raya kauyuka, da kuma ci gaba da zamanintar da aikin gona. Don haka, abinci shi ne tushen rayuwa, amma ba makami na siyasa ba. (Ibrahim Yaya daga Beijing, China)