logo

HAUSA

A yi kokarin gina wata kyakkyawar duniya inda tsirrai da dabbobi da dan Adam ke rayuwa tare cikin lumana

2022-06-08 09:59:10 CMG Hausa

Ana bikin ranar kiyaye muhalli ta duniya ne, a ranar 5 ga watan Yunin kowa ce shekara, ranar da MDD ta kebe don kara ilimantar da jama’a da ma daukar matakan da suka dace don kare muhallin duniyarmu daga gurbacewa.

An dai fara bikin ranar ce a shekarar 1974 a brining Spokane na kasar Amurka. Haka kuma rana ce da ake kara yin kira ga jama’a kan batutuwan da suka shafi muhallinmu, kamar gurbatar teku, da yawan jama’a a duniya, da batun dumamar yanayi, da farauta ko kashe namun dajin dake fuskantar barazanar karewa daga doron kasa da sauransu.

A kowa ce shekara, akan bijiro da shirye-shirye da take da ma dandalolin ganawa, inda kungiyoyi masu zaman kasu da al’ummomi da gwamnatoci ke halarta, tare da gabatar da irin manufofi da matakai mafiya dacewa da suka dace a dauka don alkinta muhallin duniyarmu.

Masana sun yi kashedin cewa, idan har ba a dauki matakan da suka dace ba, nan zuwa shekarar 2050, yawan al'ummun duniya da za su rasa matsugunnin su sakamakon bala'u masu nasaba da sauyin yanayi, zai kai mutum miliyan 143.

Masu fashin baki na kara jaddada cewa, lokaci ya yi da jama’a za su kara mayar da hankali wajen kiyaye aikata dukkan abubuwan da za su kai ga lalata muhallin duniyarmu, duba da yadda wasu kasashe kasar kasar Sin ke cika alkawuran da suka yi game da kiyaye muhalli a fannoni daban-daban, kamar kara samar da makamashin da ake iya sabuntawa, da shuka bishiyoyi, da rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli da dai sauransu. (Saminu, Ibrahim /Sanusi Chen)