logo

HAUSA

Sakatare Janar na MDD ya yi tir da harin da aka kai wata mujami’a a Nijeriya

2022-06-07 10:35:03 CMG Hausa

 

Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya yi tir da harin da aka kai wata mujami’a, ranar Lahadi a jihar Ondo dake Nijeriya, lamarin da rutsa da mutane da dama.

Cikin wata sanarwar da kakakinsa Stephane Dujarric ya fitar, Antonio Guterres ya yi tir da kausasan kalamai kan harin na mujami’ar katolika ta St Francis dake garin Owo na jihar Ondo, yana mai bayyana shi a matsayin na mugunta. Ya ce harin ya yi sanadin mutuwar mutane da jikkatar wasu da dama yayin da suke ibada.

Sakatare Janar din ya jaddada cewa, hari kan wuraren ibada, abu ne da bai dace ba. Yana mai kira ga hukumomin Nijeriya kada su yi kasa a gwiwa wajen hukunta wadanda ke da hannu.

Har ila yau, Guterres ya jajantawa iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su, yana mai yi wa wadanda suka jikkata fatan samun lafiya. Bugu da kari, ya jajanta tare da bayyana goyon bayansa ga gwamnati da al’ummar Nijeriya. (Fa’iza Mustapha)