Sulaiman A. Sani Danguguwa: Ina son samun damar karatu a China!
2022-06-07 16:05:49 CMG Hausa
Sulaiman A. Sani Danguguwa, matashi ne dake zaune a jihar Kanon tarayyar Najeriya, wanda ke matukar sha’awar koyon yaren Sinanci gami da al’adun kasar Sin.
A yayin zantawar sa da Murtala Zhang, Sulaiman Sani Danguguwa, ko kuma Li Changyuan a yaren Sin, ya bayyana dalilin da ya sa ya fara kaunar yaren Sin, da kuma yadda yake kokarin karatun yaren. Li Changyuan ya kuma bayyana fahimtarsa game da al’adu da kuma halayen mutanen kasar Sin. (Murtala Zhang)