logo

HAUSA

Mutane 38 sun rasu yayin harin da aka kai wani kauyen dake DRC

2022-06-07 10:58:12 CMG Hausa

Rundunar sojin gwamnatin kasar Kongo (Kinshasa), ta tabbatar da cewa, dakarun kawancen demokuradiyya dake adawa da gwamnatin kasar Uganda, sun kai wa wani kauyen dake jihar Ituri ta kasar Kongo (Kinshasa) hari, a daren Lahadin da ta gabata.

Kakakin rundunar, Jul Ngongo wanda ya ba da tabbacin, bai sanar da hakikanin adadin mutanen da suka rasa rayukansu yayin harin ba, amma ya bayyana cewa, sojojin kasarsa suna kokarin farautar maharan.

Wani da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin cewa, a kalla fararen hula 38 sun rasu sakamakon harin da aka kai kauyen, kuma dakarun sun kone gidaje kusan 30 a kauyen.

Tun bayan da gwamnatin kasar Uganda ta fatattaki dakarun kawancen demokuradiyya na kasar a karshen shekarun 1990, sai suka gudu zuwa yankin dake gabashin kasar Kongo (Kinshasa), inda suke gudanar da ayyukan adawa da gwamnatin Uganda, tare kuma da kai hari ga sojojin Kongo (Kinshasa), da fararen hular kasar, da kuma sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD dake kasar. (Jamila)