Manufofin Amurka na "Monroe Doctrine" ba zai samu karbuwa ba
2022-06-06 22:58:13 CMG Hausa
“Wannan taron kolin kasashen nahiyar Amurka, mai yiwuwa wata alama ce dake nuna raunin tasirin shugabancin Amurka a yankin Latin Amurka." Wata kafar yada labaran kasar Mexico ce ta yi wannan sharhin. Taron kolin kasashen nahiyar Amurka karo na tara wanda aka tsara gudanawar a birnin Los Angeles a yau Litinin 6 ga watan Yuni, sai dai kuma yadda shugabannin kasashen yankunan Amurka da dama suka yi suka tare da yin kiraye kirayen kauracewa halartar taron, da kuma matakin karshe da Amurka ta dauka na kin gayyatar kasashe kamar su Cuba, Venezuela da Nicaragua zuwa taron, duka wasu alamu ne dake nuna cewa taron kolin shiyyar wanda Amurka ke jagoranta zai iya kasancewa a matsayin wata tattaunawa ce marar fa’ida.
Tun da jimawa, shugabannin Mexico, da Bolivia, da sauran kasashe, sun taba bayyana cewa, muddin Amurka ta gaza gayyatar dukkan shugabannin kasashen nahiyar Amurkan, to su ma ba za su amsa gayyatar halartar taron kolin ba. Kasashen yankin Latin Amurka sun gabatar da tambaya dake cewa, shin ko Amurka tana son shirya “taron kolin kasashen nahiyar Amurka ne” ko kuma “taron kolin kasar Amurka"?
A watan Nuwamban 2013, a yayin da sakataren harkokin wajen Amurka na wancan lokacin John Kerry, ya gabatar da jawabi a taron kungiyar hada kan kasashen nahiyar Amurka, yayi ikirarin cewa, “zamanin manufar Amurka ta Monroe Doctrine ya zo karshe" , kuma ya kamata kasar Amurka ta yi la’akari da kasashen yankin Latin Amurka “a matsayin abokan hulda na daidai wa daida". Sai dai, da alama hakan bai sauya komai ba. A wannan lokaci, kasar Amurka tana amfani da wannan damar karbar bakuncin taron kolin kasashen nahiyar Amurkan domin kawar da “bijirewar” da take fuskanta daga wasu bangarorin kasashen Latin Amurka, wanda wannan shi ne misali na baya bayan nan dake nuna har yanzu Amurkar tana rike da manufar "Monroe Doctrine" a matsayin tunaninta.(Ahmad Fagam)