logo

HAUSA

An kashe mutane da dama a harin coci a kudu maso yammacin Najeriya

2022-06-06 09:52:36 CMG Hausa

Wasu ’yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun kashe masu ibada da dama, bayan wani harin da suka kaddamar kan wata coci dake jihar Ondo, a shiyyar kudu maso yammacin Najeriya a ranar Lahadi, kamar yadda wasu majiyoyi da dama suka tabbatar.

Harin ya faru ne a garin Owo dake jihar Ondo a yayin da masu bauta suka taru a cocin da sanyin safiyar ranar Lahadi, kamar yadda majiyoyi da dama suka bayyana.

Wani jami’in gwamnati wanda ya nemi a sakaye sunansa ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua ta wayar tarho cewa, da farko ’yan bindigar sun yi amfani da abubuwan fashewa ne a kusa da cocin, kafin daga bisani suka yi harbe-harben kan mai uwa da wabi, inda suka kashe masu bautar da dama.

Gwamnan jihar Ondu, Arakunrin Akeredolu ya tabbatar da faruwar harin, sannan ya bayyana cewa, ya yi matukar kaduwa bisa faruwar harin wanda ya yi sanadiyyar rayukan mutanen garin Owo wadanda ba su ji ba su gani ba, da kuma masu bautar a cocin St. Francis Catholic Church.

Akeredolu ya bukaci mazauna yankin da su kwantar da hankulansu yayin da aka tura jami’an tsaro domin sanya ido da kuma daidaita al’amurra a garin. (Ahmad)