logo

HAUSA

Mali: An kafa mahakar ma’adinin Lithium ta Goulamina

2022-06-06 11:09:20 CMG Hausa

Lamine Seydou Traore, ministan kula da ma’adinai, makamashi da yin amfani da ruwa na kasar Mali, ya bayyana a kwanan baya cewa, a ranar 3 ga wata ne aka fara kafa mahakar ma’adinin Lithium ta Goulamina da ke kudancin kasar a hukumance.

Ministan ya bayyana a kafofin sada zumunta cewa, za a shafe shekaru fiye da 20 ana aikin hakar ma’adinin Lithium a wannan mahakar da aka kafa, lamarin da zai sanya kasar Mali ta zama kasa ta uku a duniya a fannin samar da ma’adanin Lithium.

Bisa rahoton nazari da aka gabatar a watan Disamban shekarar 2021 dangane da yiwuwar gudanar da shirin, ana sa ran za a iya hakar ma’adinin Lithium ton 726 a kowace shekara a mahakar ma’adinin Lithium ta Goulamina. An kiyasta cewa, yawan ma’adinin Lithium mafi yawa da za a haka a shekara guda zai kai ton dubu 880. Mahakar zata kasance daya daga cikin wuraren hakar ma’adinin Lithium mai inganci mafi girma a duniya, wadanda ba a kai ga yin amfani da su ba tukuna. (Tasallah Yuan)