Yadda take kulawa da bukatun kasashe masu tasowa ya sa kasar Sin ta zama aminiyarsu
2022-06-06 20:41:22 CMG Hausa
A kwanan baya, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya ziyarci wasu kasashe tsibirai dake yankin tekun Pasific, daga bisani ya bayyana cewa, “ Kar a bar kasashe marasa karfi su ci gaba da fama da matsalar koma bayan tattalin arziki.” Maganarsa ta nuna bukatar kasashe masu tasowa ta neman samun ci gaba da wadata, da kuma dalilan da suka sanya kasar Sin ke samun goyon baya daga kasashe masu tasowa, wato saboda yadda take kulawa da bukatunsu.
Wani bayani da wata kwararriya a fannin tattalin arziki ta kasar Kenya Anzetse Were ta rubuta, wanda aka wallafa a shafin yanar gizo na mujallar Diplomat ta kasar Amurka a kwanan baya, shi ma ya tabbatar da gaskiyar ra’ayina. Wannan bayani mai taken “Sirrin kasar Sin game da manufarta da ta shafi tattalin arzikin kasashen Afirka” ya nuna dalilin da ya sa kasashen Afirka suke nuna goyon baya ga kasar Sin.
Da farko dai, a cewar Madam Anzetse, kasar Sin tana nuna daidaito ga kasashen Afirka.
Saboda yadda take bin manufofi na “zama daidai wa daida”, da “rashin tsoma baki a harkokin cikin gida na sauran kasashe”, kasar Sin ba ta taba neman yin shisshigi a nahiyar Afirka ba, ko kuma tilastawa kasashen Afirka bin tsarinta. Yayin da a nasu bangaren, kasashen yamma suna tsammanin cewa, ya kamata kasashen Afirka su bi dukkan shawarwarinsu, ko da yake, sun taba yi wa nahiyar mulkin mallaka.
Na biyu shi ne, domin kasar Sin tana girmama ‘yancin kasashen Afirka na yin zabi bisa ra’ayin kansu.
Bayan da kasashen Afirka sun yi kira da a ba su karin damammaki na yin ciniki maimakon ba da tallafi kawai, kasar Sin ta amshi kiran a farko. Daga bisani, kasar Sin da kasashen Afirka sun fi mai da hankali kan hadin gwiwar tattalin arziki, da raya bangaren kayayyakin more rayuwa, da sauran batutuwan da suka fi janyo hankalin kasashen Afirka. Yayin da a nasu bangare, kasashen yamma suke kallon kansu a matsayin abin koyi ga kasashen Afirka, ko da yake tsarinsu na raya tattalin arziki na fuskantar dimbin matsaloli, da suka hada da rashin daidaituwa tsakanin al’umma, da yawan samun tashin hankali, da masu fama da talauci, da dai sauransu.
Na uku, shi ne kasar Sin ta fahimci yanayin da kasashen Afirka ke ciki.
Saboda kasar Sin ta taba kasancewa a yanayi iri daya da kasashen Afirka, a fannin ci gaban tattalin arziki, don haka ta fahimci bukatun kasashen Afirka sosai. Wannan dalili ya sa hadin gwiwarta da kasahsen Afirka ke samar da dimbin alfanu ga kasashen. Misali, aikin gina kayayyakin more rayuwa a Afirka da kasar Sin ta zuba jari a ciki yana taimakawa rage gibin da ake samu tsakanin yankunan Afirka a fannin tattalin arziki, da rage tsawon lokacin da ake warewa da makamashin da ake konawa wajen yin zirga-zirga, da samar da dimbin guraben aikin yi, da damammaki na ciniki, da mika sabbin fasahohi da ilimi masu alaka da wannan fanni ga bangaren Afirka.
Yayin da a nasu bangare, kasashen yamma suke ci gaba da tsammanin cewa, ana yabawa kan yadda suke samun ci gaban tattalin arziki, kana kasashe daban daban na son ganin wata babbar kasa daga yammacin duniya ta zama mai fada a ji a duniya, domin hakan zai tabbatar da makomar duniya mai haske. Amma a sabanin haka, yadda kasashe masu tasowa suke nuna rashin gamsuwa da tsarin kula da harkokin duniya karkashin jagorancin kasashen yamma, shi ma ya kasance daya daga cikin manyan dalilai da suka sa kasashen Afirka ke nuna karin goyon baya ga kasar Sin, wata babbar kasa da ta sha bamban da kasashen yamma. (Bello Wang)