logo

HAUSA

ECOWAS na taron koli kan yanayin siyasar Mali, Guinea, da Burkina Faso

2022-06-05 17:48:50 CMG Hausa

Shugabannin kungiyar raya tattalin arizkin kasashen yammacin Afrika  (ECOWAS), suna taro a Accra, babban birnin kasar Ghana, domin tattauna yadda za a lalibo bakin zaren daidaita yanayin siyasar kasashen Mali, da Guinea, da Burkina Faso.

A yayin gabatar da jawabin bude taron shugabannin kasashe da gwamnatocin ECOWAS karo na shida, shugaban kasar Ghana, Nana Addo Dankwa Akufo-Addo ya ce, yana fatan kungiyar ECOWAS zata samar da hanyoyin kawo karshen dambarwar siyasa da ma rashin kwanciyar hankali dake wanzuwa a wannan shiyya.

Akufo-Addo, wanda kuma shi ne shugaban karba-karba na kungiyar ECOWAS ya ce, domin tinkarar wadannan batutuwa marasa dadi, babban burin da suka sanya a gaba shi ne, lalibo hanyoyin da zasu taimakawa wadannan kasashe, don samun nasarar maido da doka da oda.

Yace, taron kolin, zai kuma mayar da hankali wajen nazartar yanayin da ake ciki a kasashen na Mali, Guinea, da Burkina Faso, dangane da cigaban da aka samu na baya bayan nan a matakan kasa da kasa da shiyya-shiyya da ya shafi wannan shiyyar, tare kuma da daukar matakan da suka dace.(Ahmad)