logo

HAUSA

AU ta bayyana damuwa kan tabarbarewar tsaro da ayyukan jin kai a yankin Sahel

2022-06-05 18:14:04 CMG Hausa

Kungiyar tarayyar Afrika AU, ta bayyana matukar damuwa game da tabarbarewar yanayin tsaro da ayyukan jin kai a yankin Sahel.

An bayyana hakan ne a sanarwar bayan taron majalisar wanzar da zaman lafiya da tsaro ta kungiyar AU, wadda aka fidda a ranar Asabar, inda kungiyar ta nuna damuwa a yayin taronta na baya bayan nan game da yanayin da ake ciki a yankin Sahel.

AU ta jaddada nuna damuwa game da karuwar barazanar ayyukan ta’addanci a yankin Sahel, inda ake alakanta karuwar matsalar ta’addancin a sakamakon yawaitar sauye sauyen gwamnatoci dake faruwa ba bisa ka’ida ba. Sannan AU ta kuma yi gargadi game da yadda ake fuskantar kalubaloli ta fannonin tattalin arziki da zaman al’umma.

Bugu da kari, kungiyar ta yabawa kokarin da dakarun tsaron hadin gwiwa na kasashe biyar na yankin Sahel (G5) ke yi, da kuma kokarin da mambobin kasashen ke yi wajen karfafa ayyukan yaki da ta’addanci, da yaki da kungiyoyin masu dauke da makamai da na bata gari a yankin Sahel, inda ta nemi a kara himma wajen samar da karin kudade da dakarun tsaro.(Ahmad)