logo

HAUSA

Ministocin harkokin wajen tsakiyar Afrika sun tattauna game da batutuwan tsaro da zaman lafiya a yankinsu

2022-06-04 16:35:54 CMG Hausa

 

Ministocin harkokin wajen kasashen yankin tsakiyar Afrika, sun fara taro jiya Juma’a a birnin Yaounden Kamaru, domin tattauna batutuwan tsaro da zaman lafiya a yankin.

Da yake bude taron karo na 53, na ministocin zaunannen kwamitin MDD mai bada shawara kan batutuwan tsaro a yankin tsakiyar Afrika, ministan harkokin wajen Kamaru, Lejeune Mbella Mbella, ya ce yankin na fama da tarin kalubalen tsaro.

Ya ce rikicin Ukraine da ta’addanci da safarar miyagun kwayoyi da laifuffuka tsakanin kasa da kasa da na intanet da amfani da kafafen sada zumunuta ta hanyoyi masu hadari abubuwa ne masu tayar da hankali da ake fama da su a yanzu.

Jami’an sun jadadda bukatar inganta matakan tsaro da karfafa gwiwar tattaunawa da fahimtar juna tsakanin kasa da kasa da zummar shawo kan tarin kalubalen. (Fa’iza Mustapha)