logo

HAUSA

MDD ta yi tir da harin da aka kaiwa ma’aikatan wanzar da zaman lafiya a Mali

2022-06-04 15:59:39 CMG HAUSA

 

MDD ta yi amfani da kakkausar murya, wajen yin tir da harin da aka kai wa rundunarta ta musamman ta kiyaye zaman lafiya a kasar Mali wato MINUSMA.  

Da safiyar jiya ne wata mota mai sulke dake jigilar sojoji karkashin shugabancin MINUSMA, ta ci karo da wani abun fashewa a kusa da garin Douentza na yankin Mopti dake tsakiyar kasar Mali, inda ma’aikatan kiyaye zaman lafiya 2 suka rasa rayukansu yayin da wani na daban ya jikkata. Dukkan ma’aikatan 3 ‘yan asalin kasar Masar ne. Wannan ne karo na 6 da aka kai hari kan jami’an MINUSMA tun bayan ranar 22 ga watan Mayun bana.

António Guterres, babban sakataren MDD ya sanar ta bakin kakakinsa cewa, yana tir da harin da kakkausar murya, tare da kira ga gwamnatin kasar Mali ta wucin gadi, ta gudanar da bincike kan harin da kuma gurfanar da wadanda ke da hannu a gaban kotu nan take.

Har ila yau a jiyan, kwamitin sulhu na MDD ya fitar da wata sanarwa da ta yi tir da harin da babbar murya. Kwamitin ya sake nanata cewa, kamata ya yi kasashen duniya su dauki dukkan matakai na yaki da barazanar da ‘yan ta’adda suke yi wa zaman lafiya da tsaro a duniya baki daya. (Tasallah Yuan)