logo

HAUSA

Masanin Ilmin Muhalli Na Zimbabwe: Hanyar Raya Kasar Sin Ba Tare Da Gurbata Muhalli Ba Ta Zama Abin Koyi Ga Duniya

2022-06-04 16:21:43 CMG HAUSA

Masanin ilmin muhalli na kasar Zimbabwe, Courage Tavenhave ya yabawa matakan da kasar Sin take dauka na raya tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasa da kuma muhalli.

Courage Tavenhave, ya bayyana haka ne yayin da ya zanta da wakilin babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin CMG a baya-bayan nan, yana mai cewa, matakan kasar Sin na neman raya kasa ba tare da gurbata muhalli ba, da kuma kyawawan fasahohinta, sun cancanci kasashen duniya su yi koyi da su.

Masanin ya bayyana cewa, a shekarun baya bayan nan, kasar Sin ta rubanya kokarinta na kara azama kan raya kasa ba tare da gurbata muhalli ba, inda ta samu gagarumar nasara a wannan fanni. Ya kara da cewa, yayin da kasar Sin take kara azama kan raya kanta ba tare da gurbata muhalli ba, tana taimakawa sauran kasashe, musamman ma kasashe masu tasowa, wajen bunkasa makamashin da ake amfani da shi ba tare da gurbata muhalli ba. Kuma kasarsa ta Zimbabwe tana daya daga cikin irin wadannan kasashe.

Masanin ya gode wa kasar Sin da ta kafa asusun hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa ta fuskar daidaita sauyin yanayi. A cewarsa, asusun ya taka muhimmiyar rawa wajen taimakawa kasashe masu tasowa ciki hadda kasar Zimbabwe, daidaita matsalar sauyin yanayi. A ganinsa, ya dace kasashen Zimbabwe da Sin su yi koyi da juna ta fuskar raya kasa ba tare da gurbata muhalli ba.  (Tasallah Yuan)