logo

HAUSA

Shugaban AU ya tattauna da shugaban Rasha game da dage takunkumai kan hatsi da samar da sulhu game da rikicin Ukraine

2022-06-04 16:37:36 CMG Hausa

 

Shugaban Tarayyar Afrika AU, kuma shugaban kasar Senegal, Macky Sall, ya tattauna da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, dangane dage takunkumai kan hatsi da bukatar dake akwai na samun mafita game da rikicin Rasha da Ukraine.

Shugaban hukumar kula da AU Moussa Faki Mahamat, wanda ya raka Macky Sall birnin Sochi da aka yi tattaunawar, ya wallafa a shafin twitter cewa, sun tattauna kan batutuwa da dama da shugaba Putin, inda suka bayyana matsayar AU game da bukatar samar da sulhu a siyasance dangane da rikicin Ukraine, tare da bayyana illarsa ga bil adama da tattalin arzki da yankin da ma duniya baki daya.

Jami’an biyu na AU, sun kuma bayyana muhimminci daddadiyar alaka mai karfi dake tsakanin Rasha da nahiyar Afrika.

Bugu da kari, sun bayyana fatan da nahiyar ke da shi na ganin an hau teburin sulhu tare da cimma yarjejeniya domin tabbatar da kwanciyar hankali da zaman lafiya a duniya. (Fa’iza Mustapha)