logo

HAUSA

AU ta bayyana damuwa game da yanayin hakkin dan Adam a Afrika

2022-06-04 16:34:52 CMG Hausa

 

Tarayyar Afrika AU, ta bayyana matukar damuwa game da matsanancin yanayin da hakkin dan adam ke ciki a nahiyar.

Kwamitin sulhu na Tarayyar ne ya bayyana damuwar cikin wata sanarwa da ya fitar jiya, biyo bayan taronsa na baya-bayan nan kan yanayin hakkin dan adam a nahiyar.

Kwamitin ya alakanta tabarbrewar yanayin tsaro da na jin kai a Afrika da batutuwan da suka shafi matsalolin sauyin yanayi da bukatun lafiyar al’umma da sauran wasu haddura, musamman a bangarori da dama, wadanda dama ba su da kwari saboda matsalolin ta’addanci da rikice-rikicen da suka haifar da karancin abinci da tilasta raba al’umma da matsugunansu.

Har ila yau, kwamitin ya bayyana damuwa game da karuwar mutane masu rauni a Afrika, musamman ‘yan gudun hijira da wadanda suka rasa matsugunansu da masu dawowa gida da masu neman mafaka, da wadanda ba su da kasar asali da wadanda suka bata da kuma yadda karfinsu na juriya ke raguwa. (Fa’iza Mustapha)