logo

HAUSA

Mataimakin shugaban Ghana ya nemi bankunan Afrika su adana zinare yayin da tattalin arzikin duniya ke cikin yanayin rashin tabbas

2022-06-03 17:11:42 CMG HAUSA

Mataimakin shugaban kasar Ghana, Mahamudu Bawumia ya yi kira ga manyan bankunan kasashen Afrika da su gina taskokin adana zinare, domin ya zama wata garkuwa, a yayin da tattalin arzikin duniya ke cikin yanayi na rashin tabbas, wanda wannan mataki zai iya tallafawa tattalin arzikin nahiyar.

Bawumia ya yi wannan kira ne a yayin bude taron baje-koli na kwanaki uku kan ma’adanai da lantarki na yammacin Afrika, wanda aka gudanar a birnin Accra, babban birnin kasar Ghana.

Ya kara da cewa, matsanancin yanayin da annobar COVID-19 da rikicin kasashen Rasha da Ukraine suka haifar, zai iya kara jefa tattalin arzikin duniya cikin mawuyacin hali a nan gaba, sakamakon katsewar tsarin samar da kaya da raguwar wasu muhimman kayayyakin yau da kullum.

Bawumia ya jaddada cewa, akwai bukatar kasashen Afrika su tsaya da kafafunsu domin fuskantar matsalolin da ka iya tinkarowa a nan gaba, sannan ya jaddada bukatar kasashen Afrika su sa kaimi wajen kokarin nemo hanyoyin warware matsalolinsu da kansu, don magance manyan kalubalolin da za su fuskanta.(Ahmad)