logo

HAUSA

Sabon yunkurin Amurka kan batun Taiwan aikin banza ne

2022-06-03 17:40:56 CMG Hausa

A ranar 1 ga wata, mataimakiyar wakiliyar kasar Amurka ta fuskar cinikayya Sarah Bianchi, ta gana da wakilin yankin Taiwan na kasar Sin ta kafar bidiyo, inda aka sanar da kaddamar da Shawarar cinikayya ta karni na 21 tsakanin Amurka da Taiwan.

Wannan matakin da Amurka ta dauka, ya saba alkawarin da ta yi a cikin sanarwoyin hadin kai guda uku a tsakanin ta da Sin, lamarin da zai lalata dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka.

Amincewa da manufar “kasancewar kasar Sin daya tak a duniya”, sharadi ne na yadda yankin Taiwan na Sin ke yin hadin gwiwar tattalin arziki da ketare. Yadda Amurka ke mai da yankin Taiwan a matsayin kasa mai mulkin kai, da kuma yunkura daddale yarjejeniya tare da mahukuntansa, ya keta manufar “kasancewar kasar Sin daya tak a duniya”, kana ya nuna wa ‘yan a-ware na Taiwan wata alamar kuskure. Lamarin da ya sake shaida cewa, abun da Amurka ta fada na sabawa abun da take yi a zahiri, inda take cin amana a kan batun Taiwan.

Batun Taiwan batu ne da ya shafi babbar moriyar kasar Sin, kana batu ne mafi muhimmanci, mafi saukin tada hankali a dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka. Kasar Sin ta riga ta bayyana cewa, idan ba a iya daidaita batun Taiwan yadda ya kamata ba, hakan zai yi illa matuka ga dangantakar da ke tsakanin bangarorin biyu.

Bayan da gwamantin Amurka mai ci ta hau karagar mulkin kasar, sau da yawa ta rika yin alkawarin tsayawa tsayin daka kan manufar “kasancewar kasar Sin daya tak a duniya”, da daina goyon bayan Taiwan wajen neman samun ‘yancin kai, amma abubuwan da take yi ya sabawa hakan.

Hakika dai, abubuwan da Amurka ke yi kan Taiwan sun shaida cewa, lallai ba ta da sauran dabaru na hana ci gaban kasar Sin. Dole ne kasar Sin ta samu dinkuwa guri daya, kuma babu wanda zai iya hana hakan. Babu shakka irin tsokanar da kasar Amurka ke yi, za ta haifarwa mahukuntan Taiwan babbar hasara, kana kowa zai gane cewa, Amurka wata kasa ce mai cin amana. (Kande Gao)