logo

HAUSA

‘Yan gudun hijirar Afirka ta Tsakiya 300 sun koma gida daga Kamaru

2022-06-03 16:33:21 CMG HAUSA

A kalla ‘yan gudun hijira 300 ne suka baro jamhuriyar Kamaru domin komawa kasarsu ta asali jamhuriyar Afirka ta Tsakiya mai makwabtaka, a ranar Larabar da ta gabata, a wani shirin kwashe ‘yan gudun hijira bisa amincewarsu.

Kungiyoyin ‘yan gudun hijirar biyu, da suka hada da ‘yan gudun hijira 150 daga sansanin ‘yan gudun hijira na Gado Badzere dake yankin Lom da Djerem a shiyyar gabashin Kamaru, da kuma wasu 150 daga garin Batouri dake wannan shiyya, sun shiga motocin bas inda suka kama hanyar sake komawa mahaifarsu.

Ya zuwa karshen wannan shiri, wanda zai gudana tsakanin watan Yuni zuwa watan Satumba, ‘yan gudun hijirar Afirka ta Tsakiya 2,500 dake zaune a gabashin Kamaru, da yankin Adamawa, da kuma arewacin jamhuriyar Kamaru ne ake sa ran komawarsu gida, a cewar ministan dake lura da al’amuran yankunan kasa, Paul Atanga Nji, wanda ya jagoranci kaddamar da shirin kwashe ‘yan gudun hijirar dake sansanin Gado Badzere.

Shirin kwashe ‘yan gudun hijirar Afirka ta Tsakiya bisa amincewarsu, an fara shi ne a shekarar 2019, bayan wata yarjejeniyar da aka cimma tsakanin bangarori uku, da suka hada da gwamnatocin kasashen Kamaru da jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da kuma hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta MDD, UNHCR.(Ahmad)