Shugaban AU Macky Sall zai gana da Putin a Rasha
2022-06-03 16:17:12 CMG HAUSA
Shugaban karba-karba na kungiyar tarayyar Afrika AU, kana shugaban kasar Senegal Macky Sall, ya bar birnin Dakar da safiyar ranar Alhamis zuwa birnin Moscow, hedkwatar kasar Rasha, bisa goron gayyatar da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin, ya yi masa, kamar yadda fadar shugaban kasar Senegal ta sanar ga manema labarai.
Bisa sanarwar da aka bayar wa manema labaru, an ce, Sall wanda ya samu rakiyar Moussa Faki Mahamat, shugaban gudanarwar kungiyar tarayyar Afrika, zai gana da mai masaukinsa a ranar Juma’a a birnin Sochi.
Manufar ziyarar Sall ita ce, neman yadda za a sayar da hatsi da kuma takin zamani zuwa ketare, wadanda matsalar rashin fitar da su din take shafar kasashen duniya, musamman ma kasashen Afrika, da kuma yin tattaunawa kan yadda za a daidaita rikicin dake tsakanin kasashen Ukraine da Rasha.
A hannu guda kuma, kungiyar AU ta kuma amince da bukatar da shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya gabatar, inda ya aika da sako ga kungiyar tarayyar Afrikan a lokacin wani taro ta kafar bidiyo.(Ahmad)