logo

HAUSA

Sin na fatan za a shawo kan kalubalen tashe tashen hankula a jamhuriyar dimokaradiyyar Congo ta hanyar tattaunawa

2022-06-02 20:30:22 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya ce yayin da dauki ba dadi ke kara tsananta, a gabashin jamhuriyar dimokaradiyyar Congo, Sin na fatan sassan da lamarin ya shafa za su kai zuciya nesa, su kuma shawo kan rikicin ta hanyar tattaunawa da lumana.

Zhao Lijian, wanda ya bayyana hakan a Alhamis din nan, yayin da yake amsa tambayar da aka yi masa don gane da batun, ya ce shawo kan wannan rikici zai maido da daidaito a yankin da kasar take.

Ya kara da cewa, Sin ta damu matuka da yadda yanayin tsaro ke tabarbarewa a yankin, tana kuma jinjinawa duk wani yukuri na ingiza zaman lafiya da ci gaba a yankin gabashin Congo, kuma a shirye take ta taka muhimmiyar rawa, tare da sauran sassan kasa da kasa, wajen shawo kan rikicin dake addabar gabashin jamhuriyar dimokaradiyyar Congo.   (Saminu)