Yaki Da COVID-19 A Shanghai: Kwalliya Ta Biya Kudin Sabulu
2022-06-02 20:05:54 CMG Hausa
Tun bayan fara aiwatar da matakan kullen annobar COVID-19 da ta barke a birnin Shanghai na kasar Sin, kimanin watanni 2 da suka gabata, a yanzu haka mahukuntan birnin mai yawan al’umma sama da miliyan 25, sun ce matakan da aka dauka sun haifar da “da mai ido”, kuma “kwalliya ta biya kudin sabulu”.
Tuni dai aka sanar da tsara sake bude birnin, inda ake sa ran daga Alhamis din nan 2 ga watan Yuni, za a bude hanyoyin shiga unguwanni, kana za a dawo da ayyukan sufuri da zirga-zirgar ababen hawa, wadanda dukkanin su matakai ne dake nuna birnin ya farfado daga barkewar wannan annoba.
Bisa shaidu na zahiri, babbar manufar kasar Sin ta gaggauta kawar da cutar COVID-19 baki daya da zarar an gano bullar ta, ta taimakawa kasar matuka, wajen dakile bazuwar wannan annoba a sassan kasar daban daban. Mun ga yadda wannan dabara ta takaita yaduwa annobar a iya wasu birane da yankuna da aka taba samun bullarta, aka kuma shawo kan ta cikin nasara.
Muna iya tuna yadda aka aiwatar da wannan tsari a biranen Wuhan, da Zhengzhou, da Fuzhou, da Suzhou, Tianjin, da Shenzhen da Xi’an, yayin da shi ma birnin Beijing ke kara kaimin shawo kan daidaikun alkaluman bazuwar cutar, musamman ma nau’in Omicron mai saurin yaduwa.
Bahaushe kan ce “Mahakurci mawadaci”, ko shakka babu, babban darasin da duniya za ta ita koya daga wannan yanayi shi ne, jurewa matakan killace wuraren da annobar COVID-19 ta yadu cikin su, da gudanar da gwaji akai akai, da karbar rigakafi, karkashin babbar manufar da Sin take amfani da ita, ta gaggauta kawar da cutar a duk inda ta bulla baki daya, sune dabaru mafiya dacewa na shawo kan annobar COVID-19 a duniya baki daya, kuma kin bin wadannan matakai, ba abun da yake haifarwa sai asarar rayuka, da gagarumin koma bayan harkokin rayuwa baki daya.(Saminu Alhassan)