logo

HAUSA

Masana tsaro a tafkin Chadi na taro kan sabbin dabarun yakar ta’addanci

2022-06-02 12:58:02 CMG Hausa

Kwararrun masana a sha’anin tsaro daga tafkin Chadi sun fara taron tattaunawa a jamhuriyar Kamaru a ranar Laraba, domin tsara sabbin dabarun da za a yi amfani da su wajen yakar ayyukan ta’addanci da kawo karshen barazanar da shiyyar ke fuskanta.

Leopold Maxim Eko Eko, babban daraktan cibiyar bincike ta Kamaru, ya bayyana cewa, taron kwararrun karkashin wata rundunar tattara bayanan sirri ta shiyyar, wacce aka kirkira a shekarar 2014, domin kawar da ayyukan kungiyar ’yan ta’addan Boko Haram, taron zai nazarci matakan tsaron da aka yi amfani da su a lokutan baya a shiyyar, kana za a samar da wani muhimmin tsari, domin kai daukin gaggawa ga barazanar da ake fuskanta.

Eko ya bayyanawa ’yan jaridu a lokacin taron a birnin Yaounde, wanda babban sakatare a fadar shugaban kasar, Ferdinand Ngoh Ngoh, ya jagoranta, ya ce, ’yan ta’addan sun sauya dabarun da suke amfani da su wajen kai hare-hare, kuma wannan babban kalubale ne.

Ya bayyana a wajen taron na wuni biyu cewa, suna fatan hukumominsu za su kara samar da bayanan sirri, kuma za su dauki matakai ba tare da bata lokaci ba, ba kawai wajen yin kunnen doki game da dabarun da ’yan ta’addan ke amfani da su ba, har ma da murkushe su baki daya. Ya kamata a aiwatar da sabbin dabarun da aka bijiro da su a wajen tattaunawar, domin magance dukkan matsalolin tsaron da ake fuskanta. (Ahmad)