logo

HAUSA

Yadda Hadin Gwiwar Sin Da Afirka Ke Kara Ci Gaban Kasashen Afirka

2022-06-01 15:38:28 CMG HAUSA

Layin dogo yana daya daga cikin muhimman ababen more rayuwa da kasashen nahiyar Afirka suka amfana da shi, karkashin hadin gwiwar Sin da kasashen na Afirka, baya ga hanyoyin mota, da gadoji na zamani, da makarantu da cibiyoyin lafiya da makamantansu.

Tun bayan kaddamar da layin dogo na zamani na SDR a ranar 31 ga watan Mayun shekarar 2017 tsakanin Mombasa zuwa Nairobo, da kasar Sin ta gina, shekaru biyar da suka gabata, yanzu haka kasar Kenya ta shiga wani sabon tsari na rayuwa, inda ya sauya harkokin sufuri, da kasuwanci da nishadi a kasar Kenya.

Bayanai na nuna cewa, layin dake tafiyar da jiragen kasa na fasinja guda shida a kullum, ya yi nasarar jigilar fasinjoji sama da miliyan 7.7 a cikin shekaru biyar din da suka gabata. Kana a cikin watanni biyar na farkon shekarar 2022, adadin fasinjojin da aka yi jigilar su ta hanyar layin dogon na zamani, ya kai 962,000, wanda ya kai kashi 63 cikin dari a duk shekara.

Haka kuma, a cikin shekaru biyar da suka gabata, layin dogon ya yi jigilar sama da Tan miliyan 1.7 na kwantenoni. Kana yawan kayayyakin da jirgin kasan dakon kaya ya yi jigilarsu a cikin watanni biyar da suka wuce, ya kai tan miliyan 2.54, karuwar kashi 8.3 bisa dari a shekara.

Layin dogon ya kuma samar da wata kafa ga matasan Kenya, wajen bunkasa fasaha da sana'o'insu da samun kudin shiga, da inganta fasaha da samar da aikin yi da raya manyan sassan tattalin arzikin kasar kamar aikin gona, da masana'antu da yawon shakatawa.

Baya ga layin dogo tsakanin Mombasa da Nairobi, akwai na Tanzaniya zuwa Zambia (Tazara) da wadanda Sin ta gina a sassan daban-daban na Najeriya da sauran kasashen Afirka, kuma duk sun taimaka wajen saukaka jigilar jama’a da hajoji tsakanin kasashen nahiyar, baya da samar da guraben ayyukan yi da karin kudaden shiga ga mazauna wadannan yankuna, galibi matasa.

Sabon dakin taro na zamani da kasar Sin ta samar da kudin ginawa da aka kaddamar a Zambia a baya-bayan nan, ya kara nuna cewa, alakar Sin da Afirka, alaka ce ta amintakar kut-da kut da mutunta juna da samun nasara tare. Kuma duk kokarin da wasu kasashen yamma ke yi na neman illata wannan dangantaka, ba zai taba yin nasara ba. (Ibrahim Yaya)