logo

HAUSA

Gambia ta sanya hannu kan yarjejeniyar diflomasiyya da kasuwanci da Equatorial Guinea

2022-06-01 19:02:32 CMG HAUSA

Kasar Gambia dake yammacin Afirka, ta sanya hannu kan wasu yarjejeniyoyi da kasar Equatorial Guinea domin bunkasa huldar kasuwanci da diflomasiyya.

Wata sanarwa da fadar gwamnati ta Gambia ta fitar jiya Talata, ta bayyana cewa shugaban kasar Adama Barrow da ke halartar taron kolin kungiyar Tarayyar Afirka (AU), da mai masaukin baki takwaransa na kasar Equatorial Guinea Teodoro Obiang Nguema Mbasogo ne suka sanya hannu kan yarjejeniyoyin a ranar Lahadin da ta gabata,

Sanarwar ta ce, bangarorin biyu sun sanya hannu kan sanarwar bayan taro ta hadin gwiwa kan kulla huldar diflomasiyya, da yarjejeniyar hadin gwiwa da kuma yarjejeniyar fahimtar juna kan shawarwarin diflomasiyya tsakanin ma'aikatun harkokin wajen kasashen, da kuma yarjejeniyar kan daukewa masu rike da fasfo din diflomasiyya da na hidima, amfani da takardar izinin shiga kasashen juna wato Visa. (Ibrahim Yaya)