logo

HAUSA

Yan ta’addan Boko Haram sun kashe sojoji 3 da fararen hula 4 a Kamaru

2022-06-01 14:33:02 CMG Hausa

Mayakan kungiyar ’yan ta’addan Boko Haram sun hallaka sojoji uku da kuma fararen hula hudu, a wani harin da suka kaddamar da sanyin safiyar ranar Talata a yankin arewa mai nisa na jamhuriyar Kamaru, kamar yadda majiyoyi daga jami’an tsaro da mazauna yankin suka tabbatar.

Wani jami’in soji, wanda ya bukaci a sakaye sunansa, ya shedawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, ’yan ta’addan dauke da muggan makamai sun isa garin Hitaoua, dake yankin da misalin karfe 3 na safiya, agogon wurin. Inda suka afkawa dakarun tsaron gwamnati, sun kashe a kalla sojoji uku da fararen hula hudu.

Sannan sun yi garkuwa da wani mutum guda.

A cewar majiyoyin yankin, an tura karin tawagar dakarun tsaro zuwa yankin, inda suka fatattaki maharan suka tsere zuwa cikin wani tsauni.

A wani hari na daban da mayakan Boko Haram suka kaddamar a shiyyar a daren Litinin, ’yan ta’addan sun raunata fararen hula hudu, kuma dukkansu iyalai guda ne dake kauyen Yabogo.

Mayakan ’yan ta’addan sun zafafa hare-haren da suke kaddamarwa kan fararen hula da sojoji a shiyyar cikin makon da ya gabata, kamar yadda rahotannin hukumomin tsaron suka tabbatar. (Ahmad)