logo

HAUSA

Birnin Shanghai ya dawo da ayyukan samar da kayayyaki yadda ya kamata

2022-06-01 20:41:48 CMG Hausa

 

Sakamakon nasarar da aka samu a yaki da cutar COVID-19 a birnin Shanghai, yanzu haka an fara dawo da ayyukan samar da kayayyaki da harkokin rayuwa daga dukkan fannoni a ranar 1 ga wata. Wannan shi ne burin al’ummar Sinawa, da ma duniya baki daya.

Bayan shafe fiye da watanni biyu ana yaki da annobar, sake dawo da harkoki a birnin Shanghai, ya shaida cewa, yadda kasar Sin ke tsayawa tsayin daka kan matakin dakile yaduwar cutar da zarar an gano ta, wani mataki ne da ya wajaba na kare jama’a daga cutar, da kiyaye samun ci gaban tattalin arziki mai dorewa. Haka kuma bisa wannan mataki, an samu sakamako mai kyau wajen yaki da cutar ba tare da kashe kudade masu yawa ba, ta yadda kare rayuka da lafiyar jama’a da dawo da tsarin harkokin rayuwa na yau da kullum.

A bangaren masana’antu, annobar ta kawo dan karamin cikas na gajeren lokaci, abin da ya fi muhimmanci shi ne yadda ya kamata su tsara shiri na dogon lokaci. Birnin Shanghai ya fitar da jerin tsauraran matakai, kamar ba da tabbaci ga aikin samar da kayayyaki, kara ba da goyon baya ta fuskar kudi, lamarin da ya taimakawa kamfanoni masu jarin waje wajen dawo da aiki, da kuma karfafa imaninsu na kara shiga kasuwannin kasar Sin.

A kowane zamani da ake ciki, kasuwa na tattare da kalubaloli iri daban daban, abin da ya kamata a yi shi ne, samun dama daga cikinsu. Game da kasuwar kasar Sin, babu shakka ta cancanci masu zuba jari su mai da ita a sahun gaba, da ma tsara shirin hangen nesa.(Kande Gao)