logo

HAUSA

Sama da masu hakar zinare 100 ne suka mutu sanadiyyar wani rikici a Chadi

2022-05-31 10:35:40 CMG Hausa

Sama da masu hakar zinare 100 ne suka mutu, yayin da wasu 40 suka jikkata, sanadiyyar rikicin da ya barke makon da ya gabata, a wajen hakar zinare na Kouri Bougoudi dake arewacin Chadi.

Kafafofin watsa labarai na kasar sun ruwaito Daoud Yaya Brahim, wani ministan gwamnati na cewa, sabani tsakanin mutane biyu ne daga bisani ya rikide zuwa gwabza fada.

Ya ce an tura wasu sojojin da sansaninsu ke Kouri Bougaoudi, dake da nisan kilomita 35 daga inda rikicin ya barke, domin wanzar da zaman lafiya.

Ya kara da cewa, an dakatar da ayyukan wurin na hakar zinare, kuma an kwashe dukkan bakin dake wurin zuwa Libya, yayin da aka kai ’yan kasar ta Chadi garin Wour.

Rahotanni sun bayyana cewa, tun daga shekarar 2017, hakar zinare a Tibesti mai tsaunika, yake ja hankalin dubban al’ummar kasar, da masu hakar zinare daga Libya da Niger da sauran kasashe makwabta. (Fa’iza Mustapha)