logo

HAUSA

An bude bikin baje kolin kayayyakin abinci na Afirka a birnin Alkahiran Masar

2022-05-31 10:04:08 CMG Hausa

An bude bikin baje kolin kayayyakin abinci na kasashen Afirka karo na 10 (AFM), a birnin Alkahiran kasar Masar, abin da ke zama wani babban bikin baje kolin kayayyakin abinci na kasa da kasa a yankin Afirka.

Bikin na kwanaki uku wanda aka gudanar da shi a cibiyar baje kolin kasa da kasa, ya janyo hankalin masu baje koli sama da 300 daga kasashe daban-daban, inda za su baje kolin sabbin fasahohi masu kayatarwa daga ko'ina cikin duniya, da kuma sabbin fasahohi da kirkire-kirkire game da samar da abinci.

A wannan shekara, bikin na AFM zai gabatar da shirin hada abokai, wanda zai mayar da hankali kan dukkan baki, don gano bukatu da abubuwan da suke sha’awa, daidaita wadannan bukatun tare da masu ba da izini da kuma shirya tarurruka a gefen bikin baje kolin.

Tariq Ameer, manajan wani kamfanin samar da abinci na kasashen waje dake aiki a Masar, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, baje kolin na taimakawa kamfanoni wajen kaucewa bata lokaci da kuma fayyace batutuwan da suke son tattaunawa.

Da yake bayani game da tarurrukan ilimi da manyan masu jawabai da kwararru suka shirya a wurin baje kolin, ya bayyana cewa, “taron zai kawo muku sabbin abubuwa da ayyuka mafi dacewa a masana'antar samar da abinci, wanda ke da amfani a gare mu matuka." (Ibrahim)