Wani filin wasan kokowa dake shaida zumuncin Sin da Afirka
2022-05-31 15:27:22 CMG Hausa
A kasar Senegal dake yammacin nahiyar Afirka, wasan kokowa na samun karbuwa sosai, ko manyan jami’an gwamnati, ko kuma fararen hula, kowa da kowa na matukar sha’awar wasan kokowa mai dadadden tarihi a kasar. Amma a cikin dogon lokaci, al’ummar kasar ba su samu filin kokowar ko daya ba. Lokaci ya zo ranar 22 ga watan Yulin shekara ta 2018, shugaban kasar Sin Xi Jinping da takwaransa na kasar Senegal, Macky Sall, sun halarci bikin mika babban filin wasan kokawa na Senegal, wanda kamfanin kasar Sin ya taimaka wajen gina shi. Irin wannan filin, ba kawai ya taimakawa al’ummar Senegal cimma burinsu na dogon lokaci ba, har ma ya zama abun shaida na dadadden zumunci tsakanin Sin da Afirka, da aikin gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya tsakanin bangarorin biyu.
A yankin karkara na Dakar, fadar mulkin kasar Senegal, akwai wani babban filin wasan motsa jiki dake jawo hankalin jama’a sosai, wanda kamfanin gine-gine na Hunan na kasar Sin wato HCEG ya gina shi cikin shekaru biyu. Filin wasan, mai fadin murabba’in mita dubu 18, zai iya daukar masu kallo kimanin dubu 20, wanda kuma shi ne filin wasan kokawa na zamani na farko a nahiyar Afirka, kana, aiki mafi girma da kasar Sin ta gudanar don tallafawa Senegal.
A ranar 22 ga watan Yulin shekara ta 2018, yayin da yake ziyarar aiki a Senegal, shugaba Xi Jinping ya halarci bikin mika filin wasan kokawar ga Senegal, inda ya yi jawabi cewa, filin wasan kokawar ya shaida zumunci mai zurfi tsakanin al’ummomin Sin da Senegal. Senegal kasa ce mai dimbin al’adu, kuma kasar Sin tana fatan yin kokari tare da Senegal don kara karewa gami da raya al’adun gargajiya, ta yadda za’a fadada hadin-gwiwar kasashen biyu a fannin al’adu.
Ma’aikatan gine-ginen kasashen Sin da Senegal sun fuskanci kalubaloli da dama a yayin da suke gudanar da aikin gina filin mai girma, ciki har da mabambantan al’adu da yare tsakaninsu. Haka kuma, kafin fara aikin, wannan wuri fadama ne, inda aka bukaci a sake gyara shi. Musamman a watan Yuli zuwa Oktoba, wato lokacin damina a Senegal, ruwan sama yana kawo tsaiko ga aikin gine-ginen. Amma ma’aikatan dukkan kasashen biyu ba su yi kasa a gwiwa ba, har sun haye wahalhalu daban-daban, da kulla zumunci mai zurfi tsakaninsu.
Ganin yadda kamfanin kasar Sin ya yi nasarar gina filin mai inganci kuma cikin lokaci, ministan wasannin motsa jiki na kasar Senegal, Matar BA ya yaba da cewa:
“Na godewa ma’aikatan gine-gine na kasar Sin saboda jajircewarsu, inda suka yi nasarar kammala aikin tare da mika mana cikin lokaci. A ganina, wannan ya zama tamkar abun koyi ga aikin raya tattalin arzikinmu.”
Sinawa kan ce, da ka baiwa wani kifi, gara ka ba shi fasahar kamun kifin, kuma irin wannan ra’ayi ya riga ya zama babban jigo na gudanar da aikin tallafawa Afirka da hadin-gwiwar Sin da Afirka. A lokacin da kasar Sin ke samar da taimakon gina filin wasan kokawa a Senegal, ma’aikatan gine-gine na Sin sun yi kokarin horas da ma’aikatan wurin. A nasa bangaren, shugaban rukunin kula da fasahohi na aikin gina filin wasan kokawa a Senegal, Wu Guangbin ya bayyana cewa:
“Akwai ma’aikatan gine-gine na Senegal da dama da suka koyi fasahohi da dama daga wannan aiki, inda kuma suka kara fahimtar ka’idojin aiki na kasar Sin. Da suka gama aikin, akwai sauran wasu kamfanonin kasar Sin gami da na sauran kasashe da suka samar musu da guraben ayyukan yi daban-daban. Ke nan ta hanyar aiki tare da mu, sun kara samun kwarewa a fannin gine-gine.”
Malick Diaby, dan Senegal ne da ya halarci aikin ginin babban filin wasan kokawa a Dakar. Ya ce yana matukar alfahari da samun wannan dama, inda ya ce:
“Ina farin ciki sosai don samun damar shiga aikin gina wannan filin wasan. Nan gaba, babu shakka zan gayawa ‘ya’yana cewa, ni da abokan aiki mun taba shiga cikin wannan gagarumin aiki, tabbas zan gaya wa ‘ya’yana.”
A yayin da yake aikin gine-gine a Senegal, kamfanin HCEG daga lardin Hunan na kasar Sin ya yi kokarin sauke nauyin dake wuyansa, don taimakawa rayuwar mazauna wurin, ciki har da samar da agajin kayan masarufi da tallafin kudi ga iyalan da suke fama da talauci, da bada taimakon sake gyara magudanar ruwa a unguwanni daban-daban, da gina filayen wasan kwallon kafa a makarantu da sauransu, al’amarin da ya sa kamfanin kasar Sin wato HCEG ya samu babban yabo da amincewa daga jama’ar Senegal.
Tun daga shekara ta 2018, ya zuwa yanzu, an riga an shirya wasannin kokawa sama da 100 a babban filin wasan kokawa dake birnin Dakar na Senegal, al’amarin da ba cika burin ‘yan wasan kasar kawai ya yi ba, har ma yana taimakawa sosai da sosai wajen kara kiyayewa da raya al’adun gargajiyar dake tattare da wasan kokawa a Senegal. Wani dan wasan kokawa a kasar, Galass, ya bayyana cewa:
“A baya, mun shirya wasannin kokawa a filin wasan kwallon kafa, amma yanzu muna matukar farin-cikin samun irin wannan babban filin wasan kokawa, wanda shi ne kyauta mai daraja gare mu, musamman matasa ‘yan wasan. Kana, ya kara ba mu kuzari da karfafa mana gwiwar ci gaba da gudanar da wasan kokowa.”
A farkon watan Nuwambar shekara ta 2021, an yi gasar wasannin kokawa karo na 9 na kasashen ECOWAS a filin wasan kokawa dake birnin Dakar na Senegal, inda wani dan wasan daga kasar Guinea Bissau ya bayyana cewa, filin wasan nan ya burge shi sosai, kuma wannan shi ne karon farko da ya ga irin wannan filin mai girma da zamani haka, ya ce yanzu ya fahimci dalilin da ya sa ‘yan wasan kokawan kasar Senegal suka kware a wasan.
Yanzu, babban filin wasan kokawa dake Dakar na Senegal, ya riga ya zama wani shahararren ginin dake alamtar dankon zumunci tsakanin Sin da Senegal, haka kuma akwai sauran wasu ayyukan hadin-gwiwa tsakanin kasashen biyu da suka kara samar da alfanu ga al’ummar Senegal, ciki har da babban dakin wasannin kwaikwayo, da babban dakin adana kayan tarihi, da asibitocin yara da lambunan motsa jiki, da kuma manyan hanyoyin mota na zamani, wadanda suka zama tamkar alamomi ga kokarin gina al’ummomin Sin da Afirka masu kyakkyawar makoma ta bai daya a sabon zamanin da muke ciki.
Duk da cewa akwai tazara sosai tsakanin kasar Sin da kasar Senegal, amma hadin-gwiwar kasashen biyu ta haifar da alfanu ga al’ummar wurin, inda ake da yakinin ci gaba da fadada hadin-gwiwa tsakaninsu a nan gaba don kara amfanin kowa da kowa.
Tun da aka shirya babban taro karo na 18 na jam’iyyar kwaminis mai mulkin kasar Sin a shekara ta 2012, ya zuwa yanzu, shugaba Xi Jinping yana matukar maida hankali kan raya huldodin Sin da Afirka, inda ya bayyana wasu muhimman manufofin gwamnatinsa na ingiza dangantakar bangarorin biyu, wadanda suka samu babban yabo daga al’ummomin nahiyar Afirka.
A nasa bangaren, shugaban kasar Senegal, Macky Sall ya bayyana cewa:
“Ina girmama shugaba Xi Jinping saboda hangen nesa da ya yi, wanda ke cike da hikima. Irin hangen nesa da yake da shi, ya bayyana ne ta hanyar bullo da shawarar ‘ziri daya da hanya daya’, wadda za ta shafi kowa da kowa a duniya, da hada kan jama’ar kasashe daban-daban, da kawo sauki ga mu’amalarsu, musamman jama’ar Afirka da Sin. Dandalin tattauna hadin-kan Sin da Afirka, wato FOCAC a takaice, daya ne daga cikin hanyoyin hadin-gwiwa mafi muhimmanci tsakanin kasa da kasa, wanda ke kunshe da kudade masu tarin yawa, don amfanawa al’ummomin kasashe daban-daban. Ina girmama wannan shawara, bari mu hada kanmu don yin kokari kafada da kafada.”
A watan Nuwambar shekara ta 2021, a wajen taron ministoci karo na 8 na dandalin tattauna hadin-kan Sin da Afirka wato FOCAC a birnin Dakar na kasar Senegal, an zartas da “muradun hadin-gwiwar Sin da Afirka zuwa shekara ta 2035”. Bisa la’akari da hakikanin halin da ake ciki, bangarorin biyu sun kara samun fahimtar juna kan manufofinsu na samar da ci gaba, inda a karon farko suka tsara shirin hadin-kai na dogon lokaci. Kuma a sabon mafari, bangrorin Sin da Afirka za su ci gaba da hada kai, don tafiya kafada da kafada. Ko shakka babu, gaba dayan al’ummomin Sin da Afirka sama da biliyan 2.7 za su zama tsintsiya madaurinki daya, don kara samar da ci gaba mai inganci, da gina al’umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya tsakaninsu. (Murtala Zhang)