Shin ‘Yan Siyasan Amurka Sun Cancanci Kiran Kansu Masu Rajin Kare Hakkin Dan Adam Idan Ba Su Kare Kananan Yaransu Ba?
2022-05-31 21:39:30 CMG HAUSA
Yau mako guda da ya wuce, a kalla kananan yara 19 da baligai 2 sun rasa rayukansu, yayin harbe-harben da aka yi a makarantar firamare ta Robb a kasar Amurka, lamarin da ya girgiza Amurka da ma duk duniya baki daya. Jaridar “The New York Times” ta yi suka da cewa, Amurka ba kasa ce mai wayewar kai ba, saboda ba ta son kare kananan yara.
Yadda ake kulawa da kananan yara, ya nuna wayewar kan wata kasa, da kuma yadda wata kasa take kiyaye hakkin dan Adam. A matsayinta na kasa mai matukar karfi daya kacal a duniya, Amurka ta dade da gaza kiyaye kananan yara. Shin ‘yan siyasan Amurka sun cancanci kiran kansu masu rajin kare hakkin dan Adam? Sun cancanci tabo maganar demokuradiyya?
Nuna karfin tuwo ta hanyar amfani da bindiga, ya dade yana adabbar al’ummar Amurka, wanda kuma shi ne mummunan sakamakon da ya biyo bayan lalacewar doka da oda, ya kuma tsanantar matsalar wariyar launin fata, da aiwatar da doka ta hanyar da ba ta dace ba. Amma duk da ganin harbe-harben da ake yi a kasarsu, ‘yan siyasan Amurka ba su yi komai ba sai addu’a, da kokarin kwantar da hankalin al’umma, sun kuma ba da jawabai.
Kwanaki 3 bayan harbe-harben da aka yi a makarantar firamare ta Robb, a birnin Houston, wanda ke kusa da makarantar, hadaddiyar kungiyar mau rajin kare ikon mallakar bindiga ta Amurka, ta gudanar da taron shekara-shekara kamar yadda ta tsara.
Idan an mayar da iko da kudi a gaban rayukan mutane, tabbas abubuwan tausayi masu dimbin yawa za su auku. Tsarin demokuradiyya irin na Amurka bai kare fararen hula ba. Lallai tun tuni Amurka da ke kiran kanta mai rajin kare hakkin dan Adam, ba ta cancanci matsayinta ba. (Tasallah Yuan)