Amurka Da Australia Ne Kadai Suka Nuna Damuwa Game Da Hadin Gwiwa A Tsakanin Sin Da Kasashe Tsibiran Tekun Pasifik
2022-05-31 20:28:32 CMG HAUSA
Ranar 30 ga wata, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar da jawabi a rubuce, ga taron ministocin harkokin wajen Sin da tsibiran tekun Pasifik karo na biyu, inda ya yaba da kyakkyawan hadin gwiwar da ke tsakanin kasar Sin da kasashe tsibiran tekun Pasifik, wadda ta zama misali a fannonin yin hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa, da samun moriyar juna da nasara tare.
Wang Yi, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Sin yana ziyarar aiki a kasashe tsibiran tekun Pasifik. Ziyararsa ta jawo hankalin kasashen Amurka da Australia da wasu kasashen yammacin duniya, wadanda suka dade suna mayar da kasashe tsibiran tekun Pasifik kamar lambunansu, ko kuma wuraren da ke karkashin shugabancinsu, sun hana wadannan kasashe su zabi kasashen da za su hada kai da su da kansu.
A yayin taron ministocin harkokin wajen kasar Sin da kasashe tsibiran tekun Pasifik a wannan karo, kasar Sin ta sanar da ci gaba da kyautata sabbin dandali guda 6, na yin hadin gwiwa ta fuskar rage talauci, da sauyin yanayi, da kandagarkin bala’u, da aikin gona, da cibiyar ciyayin Juncao, wadanda suka biya bukatun kasashe tsibiran tekun Pasifik. Saboda haka ne ma shugabanni, da ministocin harkokin wajen kasashe tsibiran tekun Pasifik masu halartar taron, suka nuna fatansu na fadada yin hadin gwiwa da kasar Sin, a kokarin ganin jama’arsu sun kara jin dadin zamansu.
Zurfafa hadin kan kasar Sin da kasashe tsibiran tekun Pasifik, yana taimakawa wajen samun zaman lafiya, da kwanciyar hankali, da ci gaba a yankin Asiya da tekun Pasifik, lamarin da ya nuna cewa, kasashe manya da kanana suna cudanya da juna cikin adalci, suna hada kansu, suna samun nasara tare.
Ya fi kyau kasashen Amurka da Australia su daidaita bukatun kasashe tsibiran tekun Pasifik a tsanake, su dauki hakikanin matakai kamar yadda kasar Sin take yi domin raya wadannan kasashe, a maimakon nuna damuwa kan hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da kasashe tsibiran tekun Pasifik kawai. (Tasallah Yuan)