logo

HAUSA

Layin dogo na zamani da kasar Sin ta gina a Kenya yana kara karfin ci gaban Kasar

2022-05-31 11:58:42 CMG HAUSA

 

A halin yanzu, kasar Kenya ta samu wani sabon tsarin rayuwa a layin dogo da kasar Sin ta gina, tun bayan kaddamar da shi a ranar 31 ga watan Mayun shekarar 2017.

Layin dogon da ya tashi daga Mombasa zuwa Nairobi, wanda kasar Sin ta samar da kudaden gina shi, kana kamfanin gina hanyoyi da gadoji na kasar Sin mai suna (CRBC) ya gina, aka kuma fara aikin a shekarar 2014, aka kammala shi a shekarar 2017, ya zama wani abin nazari kan sauyin harkokin sufuri, da kasuwanci da nishadi a kasar Kenya.

Bayanai daga Afristar na nuna cewa, ma’aikacin layin dogon na cewa, layin ya yi jigilar fasinjoji sama da miliyan 7.7 a cikin shekaru biyar din da suka gabata.

Bugu da kari, a cewar Afristar, layin dogo na Mombasa-Nairobi na tafiyar da jiragen kasa na fasinja guda shida a kullum. Yana mai cewa, a cikin watanni biyar na farkon shekarar 2022, adadin fasinjojin da aka yi jigilar su ta hanyar layin dogon na zamani, ya kai 962,000, wanda ya kai kashi 63 cikin dari a duk shekara.

Bayanai daga Afristar sun nuna cewa, a cikin shekaru biyar da suka gabata, layin dogon na zamani ya yi jigilar sama da Tan miliyan 1.7 na kwantenoni. Bugu da kari, layin dogon dake tsakanin Mombasa-Nairobi, yana gudanar da jiragen dakon kaya guda 16 a kullum, kana yawan kayayyakin da jirgin kasan dakon kaya ya yi jigilarsu a cikin watanni biyar da suka wuce, ya kai tan miliyan 2.54, karuwar kashi 8.3 bisa dari a shekara.

A cikin shekaru biyar da ya yi yana aiki lami lafiya, layin dogon na zamani, ya samar da wata kafa ga matasan Kenya, don bunkasa fasahar da sana'o'insu da samun kudin shiga mai kyau. Yayin da canja wurin fasaha da samar da aikin yi sun kasance mahimman abubuwan ayyukan layin dogo a Kenya, ingantaccen tasirinsa kan manyan sassan tattalin arzikin kasar kamar aikin gona, masana'antu da yawon shakatawa ya kasance mai fa’idar gaske a cikin shekaru biyar din da suka gabata. (Ibrahim)