logo

HAUSA

Kungiyar kwallon Kwando ta matasan kasar Sin ta shirya tunkarar wasannin neman gurbin buga gasar Olympic ta Paris ta 2024

2022-05-30 14:09:00 CRI

Kungiyar kwallon Kwando ta matasan kasar Sin, ta shirya tunkarar wasannin neman gurbin buga gasar Olympic ta kasashen duniya, wadda za ta gudana a birnin Paris a shekarar 2024.

Kungiyar ta Sin ajin maza, za ta fara wasannin neman gurbin ne, yayin da za a bude wasannin Volleyball Nations League ko VNL a watan Yuni dake tafe.

Babban kocin kungiyar Wu Sheng, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, hanya daya tilo ta samun gurbin buga gasar birnin Paris ta 2024, ita ce samun maki mai yawa yayin wasannin dake tafe.

Kafin gasar Paris ta 2024, kungiyoyi mafiya maki za su taka babbar rawa wajen tabbatar da matsayin su, sakamakon sauyi da hukumar FIVB ta gudanar a tsarin tantance kungiyoyin da za su samu gurbin buga wasannin kasa da kasa.

A matsayin ta na kasa mai karbar bakuncin gasar, Faransa na da gurbi a gasar ajin maza da tama. Sauran gurabe 11 da suka rage kuwa na ajin maza da mata, za a zabi 6 daga cikin su ne daga wasanni 3 na neman gurbi, a watan Satumba da Oktoba na shekarar 2023.

Kana gasannin neman gurni 3, za su bawa kungiyoyi 8 damar fafatawa cikin wannin 24 bisa jadawalin da hukumar FIVB ta fitar, wanda za a fara buga ajin maza na gasar tun daga ranar 12 ga watan Satumbar 2022, da kuma 17 ga watan Oktoba 2022 domin wasannin ajin mata.

Kungiyoyi 2 a duk gasannin da suka yi nasara, su ne za su kai ga buga gasar Paris ta 2024. Sauran guraben gasar Olympic 5 kuwa, hukumar FIVB ce za ta fitar da mafi samun maki a cikin su a watan Yunin 2024, inda za ta fi baiwa kasashe daga nahiyoyin da ba su samu gurabe ba, damar shiga gasar ta Olympic.

Yanzu haka dai kungiyar kwallon Kwando ta Sin na samun horo a birnin Jiangmen, na lardin Guangdong domin tunkarar gasar VNL, inda za su kara da kasar Iran.

Game da hakan, Koci Wu ya ce "Za mu yi iya kokarin mu a gasar VNL, da ma gasar cin kofin duniya, ta yadda za su samu isassun maki da zai ba mu ikon shiga gasar Olympic mai zuwa".

Wu, wanda aka nada babban kocin kungiyar kasar Sin ta kwallon Kwando ajin maza a wata Oktoban shekarar 2020, ya zabi tawagar matasan ‘yan wasa mai kunshe da wadanda aka Haifa bayan shekarar 1999. Duk da rashin kwarewa a matakin gasannin kasa da kasa, kocin na cike da Imani game da kwazon ‘yan wasan sa.

Ya ce "Tsayin mu ba zai zamo matsala ba yayin da muke karawa da sauran kungiyoyin kasashen duniya, kuma da yawa daga ‘yan wasan mu na iya yin tsalle sosai, Ga misali Zhang Jingyin, na iya yin tsalle mita 3.70".

Koci Wu ya ce sabanin wasan ajin mata, wanda ke mayar da hankali ga dabarun wasa, a bangaren maza gasar ta fi mayar da hankali ga tsayin ‘yan wasa, da saurin su, da karfi da sauran dabarun kai hari, a ragar abokan hamayya.

Wu ya ce, bayan nazartar sauran manyan kungiyoyi, masu horaswar mu sun gano cewa, kara inganta fito da kwallo daga bangaren kungiyar ta Sin, da karbar ta su ne manyan ginshikan nasarar kungiyar.

Wu ya ce "Mutun na iya sanya iyakacin karfin sa ne yayin da yake fito da kwallo ko yake karba. Mun jima muna baiwa ‘yan wasan mu horo, da tallafin karin kayan samar da horo, ta yadda za su iya koyo da inganta buga wasa a zahiri".

Kocin ya kara da cewa, baya ga kara kwarewar sarrafa kwallo, wani bangaren mai muhimmanci shi ne, wahalar gane matsayin kungiyar kasar a jadawalin kungiyoyin kasashen duniya, bayan da kungiyar ta Sin ta tsallake zuwa wasannin kasa da kasa masu yawa, sakamakon bullar annobar COVID-19. Amma duk da haka, yana yin duk mai yiwuwa domin ganin kungiyar sa ta samu gurbi a gasar Olympics ta birnin Paris.

Bugu da kari, Wu ya ce "’Yan wasa na, suna yin iya kokari a filin wasa, kuma matasan ‘yan wasa na buga kwallon kafa da ta Kwando a lokutan su na hutu, domin rage kewa da matsin rayuwa. Burin mu na samun gurbin buga gasar Olympic bai canza ba. Za mu yi matukar amfani da wannan dama yadda ya kamata".