logo

HAUSA

AU ta yi kira ga Rwanda da Congo Kinshasa da su kai zuciya nesa

2022-05-30 12:34:21 CMG Hausa

Shugaban karba karba na kungiyar tarayyar Afirka(AU) kana shugaban kasar Senegal, Macky Sall ya bayyana damuwarsa game da yanayin da ke kara ta’azzara a tsakanin Rwanda da kuma Congo Kinshasa, tare da yin kira da su kai zuciya nesa da ma daidaita matsalar ta hanyar yin shawarwari. Ya bayyana hakan ne a jiya Lahadi ta kafar sada zumunta.

A ranar 28 ga wata, rundunar sojojin tsaron kasar Rwanda ta ce, ‘yan tawayen kasar da ake kira “Democratic Forces for the Liberation of Rwanda” sun sace wasu sojojinta biyu da suke sintiri tare da tsare su a gabashin kasar Congo Kinshasa. Kafin wannan, a ranar 23 ga wata, Rwanda ta kuma bayyana cewa, sojojin kasar Congo sun kai mata farmaki tare da ji wa fararen hula raunuka. A nata bangaren, kasar Congo Kinshasa ta zargi gwamnatin Rwanda da mara wa ‘yan tawayen M23 baya, wadanda suka yi ta gwabza kazamin fada da sojojin gwamnatin Congo Kinshasa cikin makon da ya wuce, lamarin da ya raba a kalla mutane dubu 70 da muhallansu.

Kasar Congo Kinshasa dai ta dauki matakai kan Rwanda tun ranar 27 ga wata, ciki har da kiran jakadan Rwanda dake kasar da ma dakatar da zirga-zirgar jiragen saman kasar Rwanda. Shi ma kamfanin jiragen saman kasar Rwanda ta mayar da martani a ranar 28 ga wata, inda ya sanar da soke dukkanin zirga-zirgar jiragen sama zuwa biranen kasar Congo Kinshasa, ciki har da Kinshasa da Lubumbashi da sauransu.(Lubabatu)