Kar A Maimaita Kuskuren Da Aka Taba Yi Shi A Baya
2022-05-30 17:34:18 CMG Hausa
Yau 30 ga watan Mayu, rana ce ta musamman, a shekaru 55 da suka wuce ne, Chukwuemeka Ojukwu, shugaban al’ummar Igbo ta Najeriya ya sanar da ballewar yankin kudu maso gabas daga kasar Najeriya, don kafa “jamhuriyar Biafra”, lamarin da ya ta da yakin basasa a kasar. An shafe tsawon shekaru 2 da rabi ana wannan yaki, wanda ya haddasa hasarar miliyoyin rayukan mutane. A karshe dai, gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi nasarar kare cikakken yankin kasar, sai dai kamar yadda shugaban gwamnatin soja na kasar na lokacin Yakubu Gowon ya fada, “Ba wanda ya ci nasara a wannan yaki.” Sa’an nan matsalar kabilanci da yakin ya haddasa, tana ci gaba da haifar da mummunan tasiri kan harkokin siyasa, da tattalin arizki, da zaman al’umma na kasar Najeriya, har zuwa yanzu.
Idan mun waiwayi tarihi, mu kan gano shisshigin kasashen waje a cikin yakin da ke janyo baraka ga kasa. Bayan barkewar yakin Biafra, daga cikin kasashen yammacin duniya, kasar Faransa ce ta fara sayar wa “jamhuriyar Biafra” da makamai tun farkon yakin, sa’an nan kasar Portugal ta ba ta damar yin amfani da cibiyar gyaran jiragen samanta. Bayan da Chukwuemeka Ojukwu ya yi amfani da batun tamowa da matsalar tarin yawan ‘yan gudun hijira wajen neman taimako daga kasashen yamma, karin kasashe masu kudi na yammacin duniya sun samar da tallafi ga “jamhuriyar Biafra”. Sai dai Ojukwu ya yi amfani da kudaden wajen neman samun karin makamai da sojojin haya, maimakon kai dauki ga mutanen da suke fama da yunwa. A karshe dai, shissigin da kasashen waje suka yi ya tsawaita lokacin yakin, da sanya jama’ar kasar Najeriya cikin dimbin wahalhalu, da asarar rayuka da dukiyoyinsu.
Duk da haka, har zuwa yanzu, wasu kasashe ba su canza al’adarsu ta son sanya hannu cikin harkokin cikin gida na sauran kasashe ba. Har ma su kan fake da batun “hakkin dan Adam” da “dimokuradiya” da “ ‘yanci”, suna neman tabbatar da moriyar kai, yayin da suke yin shisshigi a wurare daban daban. Makarkashiyar da suka kulla ta jefa kasashe irinsu Iraki, da Afghanistan, da Syria, da Libya, da sai sauransu, cikin yanayi na fuskantar ballewar kasa da rarrabuwar kan jama’a. Wadannan kasashe suna kallon duniya tamkar wani “fili na wasa”, kana “wasannin” da suke yi su kan haddasa hasarorin rayukan jama’ar sauran kasashe, da salwantar dukiyoyinsu.
Saboda haka, wani babban aiki dake gaban kasashe masu tasowa shi ne su kare mulkin kai da ‘yancin kansu, da kokarin tabbatar da dinkuwar kasa waje guda. Ya kamata su yi kokarin dakile ra’ayin ballewar kasa, da hana munanan ayyukan ‘yan aware, gami da hana sauran kasashe yin shisshigi cikin harkokin su na cikin gida. Ta haka ne kawai za a iya magance sake yin kuskure na neman ballewar wani yanki daga wata kasa, da samun rarrabuwar kawunan al’umma, wanda aka sha yin sa a tarihin dan Adam. (Bello Wang)