logo

HAUSA

An dage dokar ta baci a fadin kasar Sudan

2022-05-30 11:03:08 CMG HAUSA

 

Shugaban gwamnatin riko na kasar Sudan Abdel Fattah Al-Burhan, ya ba da umarnin dage dokar ta baci a dukkan sassan kasar.

Wata sanarwar da gwamnatin rikon ta fitar jiya, ta ce an ba da umarnin ne, domin samar da kyakkyawan yanayin tattaunawar da za ta kai ga cimma sulhu yayin wa’adin rikon mulkin kasar.

Sudan na fama da rikicin siyasa tun bayan da shugaban rundunar sojin kasar Abdel Fattah Al-Burhan, ya ayyana dokar ta baci a ranar 25 ga watan Oktoban 2021 tare da rushe majalisar gwamnatin rikon kasar. (Fa’iza Mustapha)