logo

HAUSA

Jam’iyyar PDP a Najeriya ta zabi wanda zai tsaya mata takara a babban zaben kasar na 2023

2022-05-30 09:48:50 CMG Hausa

Ranar Asabar 28 ga watan Mayu, agogon Najeriya, babbar jam'iyyar adawa ta PDP, ta tsayar da Atiku Abubakar, a matsayin wanda zai yi mata takara a zaben shugabancin kasar a shekarar 2023.

Tun a ranar 26 ga watan Mayu ne, jam'iyyar PDP ta shirya zaben fitar da gwani, na wanda zai yi mata takarar shugaban kasa a babban birnin tarayya Abuja. Bayan kada kuri'a, Atiku Abubakar mai shekaru 75, ya samu kuri'u 371, kimanin kashi 49.3 cikin 100 na kuri’un da aka kada, inda ya zama dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar.

Idan ba a manta ba, Atiku Abubakar ya sha tsayawa takara a zaben shugabancin kasar, inda a shekarar 2019 ya fafata da dan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) kuma shugaba mai ci Muhammadu Buhari, karkashin inuwar jam’iyyar PDP, inda a karshe ya sha kaye a hannun Buhari.

Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, ta dage ranar zaben fitar da gwani a baya aka shirya gudanarwa a ranar 29 zuwa 30 ga watan Mayu da mako guda zuwa 8 ga watan Yuni. Kamar yadda jadawalin zaben Najeriya ya nuna, a ranar 9 ga watan Yuni ne, wa'adin da hukumar zaben kasar mai zaman kanta ta baiwa dukkan jam'iyyu na su mika sakamakon zaben fidda gwani na masu tsaya musu takara zai cika. A ranar 25 ga watan Fabrairun shekarar 2023 ne, za a gudanar da zaben shugaban kasa a Najeriya. (Ibrahim)