Sharhi: Me ya sa aka ce Sin ta dauki matakai daidai wajen fama da cutar COVID-19?
2022-05-30 20:43:56 CMG Hausa
Bisa sabuwar kididdigar kungiyar lafiyar duniya ta WHO ta bayar a farkon watan Mayun bana, an ce, ya zuwa karshen shekarar 2021, yawan wadanda suka mutu sakamakon cutar COVID-19 ya kai kimanin miliyan 15, ciki har da Amurkawa miliyan daya. Amma yawan wadanda suka mutu, da wadanda suka kamu da cutar a kasar Sin yana matsayi mafi kankanta.
Idan an kwatanta da sakamakon yaki da cutar da Amurka da Sin suka samu, za a gane bambancin da ke tsakanin manufar Amurka ta kin yin komai a fannin yaki da cutar, da manufar kasar Sin ta dakile yaduwar cutar da zarar an gano ta.
Dalilin da ya sa kasar Sin ta mutunta manufar dakile yaduwar cutar COVID-19 da zarar an gano ta, shi ne samun sakamako mafi kyau bisa yin hasara kadan, ta yadda za a iya tabbatar da rayuka da lafiyar al’umma, da ma gudanar da ayyukan samarwa, da ci gaban zaman yau da kullum yadda ya kamata.
Yayin da ake kokarin dakile yaduwar cutar, ana kokarin tabbatar da ci gaban tattalin arziki ba tare da tangarda ba. Idan mun yi hangen nesa, za mu gane cewa, manufar za ta taimakawa bunkasar tattalin arzikin kasar Sin cikin dogon lokaci.
Hakikanin shaidu sun nuna cewa, Manufar kin yin komai a fannin yaki da cutar COVID-19, ba ta dace da halin da kasar Sin ke ciki ba, a maimakon hakan, yadda Sin ke daukar matakai don dakile yaduwar cutar da zarar an gano ta yana da amfani sosai. Har yanzu ana fama da cutar a duk fadin duniya, akwai rashin tabbas sosai. Don haka Sin za ta ci gaba da bin manufar ta, bisa aniyar sauke nauyin al’ummarta, da ta duk duniya a baki daya. (Kande Gao)