logo

HAUSA

Najeriya: An tabbatar da harbuwar mutane 21 da cutar kyandar biri

2022-05-30 19:50:51 CMG HAUSA

 

Adadin mutanen da aka tabbatar sun harbu da cutar kyandar biri a Najeriya sun kai mutum 21, ta kuma bulla a jihohin kasar 9, inda ta hallaka mutum guda, tun bayan bullar ta a watan Janairun shekarar nan.

Cibiyar yaki da cututtuka ta Najeriya NCDC, ta fitar da wani rahoto a jiya Lahadi, wanda a cikin sa ta ce a wannan shekara, ana nazari kan mutane 66, wadanda mai yiwuwa sun harbu da cutar a jihohin kasar sama da 20.

NCDC ta ce Najeriya na cikin hadarin bazuwar cutar ta kyandar biri, bisa sakamakon binciken baya-bayan nan da aka gudanar.  (Saminu)